Kun san mutumin da ya ciji karen budurwarsa?

Chihuahua Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karen da aka kashe din ya yi kama da irin na kasar Japan ne nau'in Chihuahua

An yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari bayan da aka same shi da laifin cizon karen budurwarsa har ya cire masa kai.

An yankewa Luis Arroyo hukuncin zaman yarin ne bayan da aka same shi da laifin cin zarafin dabbar a gida.

Ranar 4 ga watan Fabrairun da ya gabata ne, Mista Arroyo mai shekara 40 ya kai wa karen dan wata biyu farmaki, kuma ya ci zarafin budurwar tasa a yammacin Lares.

Alkalin kotun Carlos Lopez Jimenez, ya kuma ci Mista Arroyo tarar dala 3,000.

A cewar jaridar El Vocero, Mista Arroyo ba shi da aikin yi kuma yana zama ne tare da budurwar tasa mai shekara 38 tsawon wata shida.

Rahotanni sun ce dan kwikuyon ya mutu ne nan take bayan da mutumin ya cije shi, amma ba a gano dalilin da ya sa ya aikata hakan ba.

Labarai masu alaka