Nigeria: Majalisa ta dakatar da Ndume, ta wanke Saraki da Melaye

Ndume Hakkin mallakar hoto NIGERIAN SENATE
Image caption Kawo yanzu Sanata Ndume bai ce komai ba

Majalisar dattawan Najeriya ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjayenta, Sanata Ali Ndume, saboda korafin da ya gabatar kan shugaban majalisar da kuma Sanata Dino Melaye.

An dakatar da shi ne bayan kwamitin da'a na majalisar ya wanke shugabanta Bukola Saraki, da Sanata Dino Melaye daga zargin shigo da mota ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da takardar shaidar digiri na bogi.

Hakan na nufin Sanatan ba zai sake shiga majalisar ba, kuma ba za a biya shi dukkan alawus din da ya saba karba ba.

Sanata Ndume ya dade yana takun saka da shugaban majalisar,amma batun ya fito fili ne bayan da aka sauke shi daga mukamin shugaban masu rinjaye.

A makon jiya ne Sanata Ndume ya nemi majalisar ta yi bincike kan labaran da Sahara Repoters ta wallafa da ke cewar Mista Saraki ya shigo da mota kasar ba bisa ka'ida.

Yayin da shi kuma aka zarge shi da yin amfani da takardar digiri na bogi.

A ranar Laraba ne kwamitin da'ar ya gabatar da sakamakon binciken wanda ya wanke Sanata Saraki da Dino Melaye daga laifufukan da aka zarge su da su a rahotannin jaridar.

Kwamitin ya kuma nemi a dakatar da Sanata Ndume daga majalisar na tsawon ranukun zaman majalisar 181.

Wasu 'yan Majalisar irin su Sanata Joshua Lidani dake wakiltar Gombe ta Kudu sun nemi a yi wa Sanata Ndume gargadi ne kawai ba tare da dakar da shi ba.

Amman wasu 'yan majalisar ba su yarda da hakan ba, suna masu cewar ba yau Sanata Ndume ya fara irin wannan laifin ba.

Daga bisani sai majalisar ta rage tsawon lokacin da za a hana sanata Ndume zuwa majalisar daga ranukun zaman majalisar 181 zuwa wata shida.

Labarai masu alaka