Ina masallaci lokacin da majalisa ta dakatar da ni — Ndume

Sanata Ali Ndume Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Kwamitin da'a na majalisar dattawan Najeriya ne ya dakatar da sanata Ndume

Sanata Muhammad Ali Ndume wanda majalisar dattawan Najeriya ta dakatar, ya ce ya tafi sallah a lokacin da majalisar ta dakatar da shi.

A ranar Laraba ne dai kwamitin da'a na Majalisar dattawan kasar ya dakatar da sanata Ndume bisa dalilin rashin cikakken bincike kafin gabatar da korafi.

Shi dai sanata Ali Ndume ya nemi da zauren majalisar ya yi bincike kan wasu labarai da jaridun kasar suka buga dangane da zarge-zarge kan shugaban Majalisa, sanata Bukola Saraki da sanata Dino Melaye.

Jaridun dai sun nuna cewa shugaban Majalisa, sanata Bukola Saraki matsa wa shugaban hukumar Kwastam, Hameed Ali, lamba ne saboda jami'an hukumar sun kama motar da ya shiga da ita kasar ba tare da biyan kudin haraji ba.

Shi kuma sanata Dino Melaye, jaridun sun nuna shakku kan kammala digirinsa daga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

To amma bayan wanke shugaban majalisar da sanata Dino Melaye daga zarge-zargen, kwmaitin da'a na majalisar ta dattawa ya zartar da hukuncin dakatar da sanata Muhammad Ali Ndume daga majalisar na tsawon watanni shida.

Ku saurari hirar sanata Ali Ndume wadda Ibrahim Isa ya yi:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Sanata Muhammad Ali Ndume

Labarai masu alaka