Na shafe shekaru ina sauraron BBC — Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya dade yana sauraron sashen Hausa na BBC

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce, ya shafe shekaru yana sauraron sashen Hausa na BBC.

Shugaban dai ya fadi hakan ne a wani sakon murya domin taya sashen Hausa na BBC murnar cika shekara 60 da fara watsa shirye-shiryensa.

Da man dai a baya Muhmamadu Buhari ya shaida wa wasu jaridu cewa a kowace safiya sai ya saurari BBC Hausa.

Shugaban ya kuma bayyana irin yadda BBC ke wayar wa da al'ummar Najeriya da Afirka ta yamma kai dangane da batutuwan yau da kullum.

Ku saurari muryar shugaban:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muhammadu Buhari, ya ce, ya shafe shekaru yana sauraron sashen Hausa na BBC.