Kalli bikin cikar BBC Hausa shekara 60 a Abuja

A ranar Alhamis ne aka yi bikin cikar BBC Hausa shekara 60 da fara aiki a Abuja.

Ummulkhairi
Bayanan hoto,

Ummulkairi Ibrahim tana hada rahoton BBC Hausa talbijin a cibiyar Shehu Musa 'Yar'adua inda aka gudanar da bikin

Bayanan hoto,

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Yakubu Dogara yana gabatar da jawabi a taron.

Bayanan hoto,

Ahmed Abba-Abdullahi (a dama) da wani bako a bikin.

Asalin hoton, BBC

Bayanan hoto,

Ibrahim Isa na bai wa ciki hakkinsa a wajen taron.

Bayanan hoto,

Muhammad Abdu Mamman Skipper yana daukar Nasidi Adamu Yahaya a lokacin da yake tattaunawa da baki kai tsaye a shafinmu na BBC Hausa Facebook.

Bayanan hoto,

Tsohon Shugaban Sashen Hausa na BBC, Mansur Liman shi ma ya halacci taron har ma ya gabatar da jawabi.

Bayanan hoto,

Tsohon Ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Maude Rabi'u Gwadabe da Ahmed Wakili Zaria.

Bayanan hoto,

Mansur Liman tare da jakadan Birtaniya a Najeriya, Paul Arkwright.

Bayanan hoto,

Daraktan BBC Media Action a Najeriya, Seamus Gallagher, da Editan BBC Hausa na Abuja, Naziru Mika'ilu.

Bayanan hoto,

Farfesa Jibrin Ibrahim da ma'aikacin BBC Muhammad Kabir Muhammad.

Bayanan hoto,

Sadiya Umar Tahir wata mai yi wa kasa hidima da BBC da Habiba Adamu ta sashen Hausa na BBC

Bayanan hoto,

Yusuf Ibrahim Yakasai ya sha manyan kaya yana cike da annashuwar wannan rana.

Bayanan hoto,

Bilkisu Babangida kenan tana sauraron jawabin da manyan baki suke gabatarwa

Bayanan hoto,

Nasidi Adamu Yahaya ya kai lomar abinci bakinsa

Bayanan hoto,

Farfesa Umaru Pate yana zantawa da manema labarai.

Bayanan hoto,

Halima Umar Saleh tana neman bakin da za ta bai wa abinci a taron