Ɗaurin rai da rai kan wanda ya kashe saniya a India

Akasarin 'yan kasar Indiya suna daukar saniya da babban matsayi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Akasarin 'yan kasar Indiya suna daukar saniya da babban matsayi

Jihar Gujarat da ke yammacin India ta zartar da wata doka da za ta yanke hukuncin daurin rai da rai kan duk mutumin da aka kama da laifin yanka saniya.

A karkashin dokar kare hakkin dabbobi, duk wanda aka samu da laifin jigilar naman shanun zai sha daurin shekara goma.

Akasarin 'yan kasar Indiya suna daukar saniya da babban matsayi, kuma jihohi da dama sun haramta kashe shanu.

Sai dai gyaran da aka yi wa dokar a Gujarat na nufin ita ce jihar da ta fi daukar tsattsauran mataki kan duk wanda ya kashe shanu.

Haka kuma za a ci tara mai tsanani ta $771 kan mutumin da aka kama da laifin kisan ko yanka shanu.

Ministan Gujarat ya shaida wa manema labarai cewa saniya wata alama ce ta al'adun India, yana mai cewa an dauki matakin ne bayan an tuntubi al'umar jihar.

Vijay Rupani ya sha jaddada cewa za a yanke hukunci mai tsauri kan duk mutumin da aka kama da laifin kashe saniya.

Za a soma aiwatar da dokar ce ranar Asabar.

Labarai masu alaka