'Za mu yi sabon gini a yankin Falasdinawa'

Netanyahu Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Benyamin Netanyahu ya ce zai yi aiki tare da shugaban Amurka, Donald Trump

Isra'ila ta sanar da cewa za ta gina sabuwar alkarya a wurin da ta mamaye da ke yammacin gabar kogin Jordan.

Ginin irinsa na farko tun bayan fiye da shekara 20 zai kasance kusa da birnin Nublus da ke makwabtaka da yankin falasdinawa.

Majalisar tsaron Isra'ilar ce dai ta yanke hakan, bayan wani taronta da ta yi a jiya Alhamis.

Za dai a ayi amfani da wannan sabuwar alkaryar ne wajen tsugunar da iyalan Yahudawan da aka tasa daga Amona, wani wuri da ke yankin na Falasdinawa wanda kuma wata kotun Isra'ilar ta ce Yahudawan na zaune ba bisa ka'ida ba.

Daman firaiministan Isra'ilar, Benyamin Netanyahu ya yi alkawarin sama wa mutanen matsuguni tun bayan hukuncin da kotun kasar ta yanke a watan Fabrairu.

Tuni dai shugabannnin falasdinawa suka yi Allah-wadai da aniyar isra'ila ta ci musu iyaka.

Sun kuma yi kira ga kasashen duniya da su yi wa tufkar hanci.

A watan da ya gabata ne dai shugaban Amurka, Donald Trump ya umarci Isra'ilar da ta dakatar da gine-gine a yankunan Falasdinawa.

Tun dai hawan mista Trump shugabancin Amurka, Isra'ilar ta kirkiro sabbin wuraren zama ga Yahudawa guda dubu shida a yankunan na Falasdinawa.

An dade ana sa-in-sa tsakanin Yahudawa da Falasdinawa kan wurin zama a yammacin gabar kogin Jordan da gabashin birnin Qudus.

Fiye da Yahudawa dubu 600 ne ke zaune a wurare 140 da ke yankunan, tun bayan mamaye su da Isra'ila ta yi a shekarar 1967.

Hakan kuwa a idanun duniya, ya kasance haramtaccen al'amari duk kuwa da musantawar da Isra'ilar ke yi.