Tumɓuke Assad ba shi ne burinmu ba a yanzu — Amurka

Nikki Haley Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tsokacin Wakiliyar Amurka Nikki Haley ya firgita 'yan adawar Siriya

Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley, ta ce Amurka ba ta da sauran burin tsige shugaban Siriya Bashar al-Assad.

Abmasada Nikki ta shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa, "Ba dole ba ne mu mayar da hankali kan tsige Assad kamar yadda gwamnatin da ta gabata ta yi."

A lokacin mulkin shugaba Barack Obama dai Amurka ta ce dole Assad ya sauka daga mulki, kuma ya goyi bayan 'yan tawayen da suke yaki da shi.

Sai dai kuma Amurkan ta raba karfinta kan abubuwa daban-daban bayan bullowar kungiyar IS, mai da'awar kafa daular Musulunci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Tillerson ne babban jami'in gwamnatin Amurka da ya ziyarci Turkiya tun bayan hawan Trump mulki

Misis Haley, ta ce, "Ba mu da burin ci gaba da mayar da hankali don ganin mun kori Assad."

Ta kara da cewa, "Burinmu shi ne mu duba yadda al'amura za su daidaita, wa muke bukata mu yi aiki da shi domin kawo wa mutanen Siriya sauyi."

Wakiliyar BBC a fadar gwamnatin Amurka Barbara Plett Usher, ta ce Misis Haley ta fito karara ta bayyana abin da dama manufar Amurkar ce ta dan lokaci.

Wakiliyar BBC ta kara da cewa, yaki da kungiyar IS a Siriya, shi ne ya zama babban abin da gwamnatin Obama ta mayar da hankali kai a shekarar da ta gabata.

Kuma shigar kasar Rasha cikin yakin a shekarar 2015 domin mara wa shugaba Assad baya, ya kawo cikas ga duk wani yunkuri da Amurka ke yi na taimaka wa bangaren da ke adawa da gwamnati.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin gwamnati Siriya na sintiri

A wata ziyara da sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya kai Turkiyya, ya ce, "Mutanen Siriya su ne za su yanke hukunci kan ci gaban Mista Assad a karagar mulki."

Sai dai wani wakilin 'yan adawar Siriya ya kira sanarwar Misis Haley da cewa, "Abin mamaki ce," ya kara da cewa wakilan Amurkan na aike wa da "sakonni masu rikitarwa."

Wani dan bangaren adawa na Siriya Farah al-Atassi, ya fada wa manema labarai a Geneva cewa, "Mun ji mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurka ta fadi sabanin abin da Mista Tillerson ke fada yau a Turkiyya".

"Sun fito fili sun fada cewa Assad ba shi da rawar da zai taka a wannan lokaci na sauyin mulki."

Shugaba Donald Trump dai, ya sha alwashin yin aiki kut-da-kut da Rasha, wacce ke goyon bayan Mista Assad da sojojinsa lokacin yakin basasar Siriya.

Labarai masu alaka