Sanƙarau ya kashe mutane da dama a Nigeria

. Hakkin mallakar hoto Planet Observer
Image caption Nau'in cutar da aka samu bana a Najeriya ba irin wanda ke samu da ba ne

A Najeriya wani sabon nau'in cutar sankarau na ci gaba da kashe mutane, inda zuwa yanzu kusan 328 sun mutu, a lokacin da ma'aikatan kiwon lafiyar kasar ke neman riga-kafin sabon nau'in cutar.

Cutar, wadda ta fara bulla a jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin kasar, ta yadu zuwa jihohi 15 na kasar.

A ranar Alhamis Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar CDC, ta ce an tabbatar da mutuwar mutum 269 sakamakon cutar.

Kazalika hukumar kiwon lafiya ta babban birnin Najeriya, Abuja, ta ce cutar ta kashe mutum biyar a birnin cikin makon nan.

Cibiyar CDC ta ce a bara war haka mutum 11 ne suka mutu sanadiyyar cutar sankarau, inda 218 suka kamu da cutar.

Saboda yawan mace-macen da sabon nau'in cutar ke janyowa cibiyar CDC ta ce za ta jagoranci matakan dakile yaduwar cutar a fadin kasar.

Wani Jami'i a ma'aikatar lafiya ta kasar Dr Sani Gwarzo, ya ce cutar ta fi kamari ne a arewacin Najeriya.

Jihohin da cutar ta shafa sun hada da Kano da Katsina da Neja da Sokoto da Kebbi da Zamfara da kuma babban birin Najeriya, Abuja.

Har wa yau jami'in ya ce an samu rahoton barkewar cutar a jihohin Gombe da Nasarawa da Taraba da Yobe da Osun da Cross River da Lagos da kuma Plateau.

Labarai masu alaka