Hotunan wasu abubuwa da suka faru a Afirka a makon nan

Zababbun wasu hotuna na wasu abubuwa da suka faru a Afirka da kuma 'yan Afrika a wasu wuraren a makon nan.

Lia Annickson Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Lia Annickson wani mai yin zane-zane a kan titi na nuna daya daga cikin zanan da ya yi a birnin Abidjan, na kasar Ivory Coast ranar Laraba.
Wasu maza suna tattaunawa a kan titin tsohon birnin Marrakech, a Kasar Morocco. Ranar Talata 28 ga watan Maris Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A ranar Talata kuwa an dauki hoton wadannan mutanen suna tattaunawa a kan titin tsohon birnin Marrakech, a kasar Morocco. T
Gabar tekun birnin Alexandria na kasar Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu mata kenan a lokacin da suke daukar hoto a ranar Lahadi, a gabar tekun birnin Alexandria na kasar Masar.
Puntland da ke kasar Somaliya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An dauki hoton wasu tumaki a garin Puntland da ke kasar Somaliya, inda ake nuna wahalar da suke sha sakamakon farin da ake fama da shi a kasar, inda ba abin da suke bukata da ya fi ruwan sha.
Wannan yarinyar 'yar kasar Somaliya ce tana tuananin za ta burge dan uwanta saboda ta sa gilashin wasa wanda ta yi shi da kwalin magani. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan yarinyar 'yar kasar Somaliya ce tana tuananin za ta burge dan uwanta saboda ta sa gilashin wasa wanda ta yi shi da kwalin magani.
'Yan kasar Laberiya sun taru ranar Juma'a a birnin Monrovia don yin bankwana ga matashin mawaki Quincy B, wanda ya rasu a hatsarin mota a cikin watan Maris yana da shekara 23. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan kasar Laberiya sun taru ranar Juma'a a birnin Monrovia don yin bankwana ga matashin mawaki Quincy B, wanda ya rasu a hatsarin mota a cikin watan Maris yana da shekara 23.
Masu tallan kayan kawa a birnin Cape Town suna rangwada sanye da kayan ado na zamani na kamfanin Botswann. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu tallan kayan kawa a birnin Cape Town suna rangwada sanye da kayan ado na zamani na kamfanin Botswann.
Wasu 'yan kasar Mali da suka halacci taron samar da zaman lafiya na kasa a birnin Bamako a ranar Lahadi, koda yake tsofaffain 'yan tawaye da jam'iyyun adawa sun kauracewa taron. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan kasar Mali da suka halacci taron samar da zaman lafiya na kasa a birnin Bamako a ranar Lahadi, koda yake tsofaffain 'yan tawaye da jam'iyyun adawa sun kauracewa taron.
Orthodox Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wadannan wasu Kiristocin Eritrea da na Habasha ne suke addu'a a wajen wani karamin Cocin mabiya darikar Orthodax a kan tsibirin Girka na kasar Lesbos a ranar Talata, bayan sun samu tsallake tekun Bahar Rum lafiya.
A handout photo made available by the World Surf League (WSL) of Jordy Smith of South Africa in action during the Drug Aware Margaret River Pro surfing event at North Point, Australia, 29 March 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wani dan Afirka ta Kudu mai wasan tsere a teku, Jordy Smith, gabanin wata gasa da za a yi a kasar Australiya a ranar Laraba.
Libyans attend a candlelit concert marking 'Earth Hour' in the eastern coastal city of Benghazi on March 25, 2017, as iconic landmarks and skylines are plunged into darkness as the 'Earth Hour' switch-off of lights around the world got under way to raise awareness of climate change. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kasar Libya a garin Benghazi na gudanar bikin Earth Hour a ranar Asabar, a wani bangare na wayar da kai kan sauyin yanayi.
A photograph made available on 27 March 2017 shows a herd of camels passing by an Internally Displaced Person (IDP) camp in the outskirts of Qardho in Somalia"s semi-autonomous region of Puntland, Somalia, 26 March 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Wadannan Rakuma na kan hanyar zuwa wani yanki mai kwarya-kwaryar cin gashin kai a Puntland a kasar Somaliya.
Athletics - IAAF World Cross Country Championships - Senior Race Women - Kololo Independence Grounds, Kampala, Uganda - 26/03/17 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kasar Uganda ta karbi bakuncin IAAF na wata gasa da aka gudanar a birnin Kamfala ranar Lahadi, wannan tsarern mata ne a gasar.

Hotuna daga kamfanonin dillancin labarai na AFP da AP da EPA da Getty da kuma Reuters

Labarai masu alaka