Ya za ka ji idan budurwarka ta biya ka kudin da ka kashe mata?

Sako daga Hakkin mallakar hoto @MissMoshiku Twitter Handle
Image caption Sakon da bankin ya aiko wa budurwar bayan da wasu wadanda suka yabi hukunci da ta yanke sun tura mata kudi a asusun bankinta

Labarin yadda wata budurwa ta mayar wa da saurayinta kudin da ya kashe mata bayan ya mata gori don ta ce ta daina son sa bayan ya kai ta cin abinci, yana ta jan hankalin mutane a shafukan sada zumuntar Najeriya.

Mutumin wanda yake yawan amfani da shafin Twitter da taken @pabloayodeji, ya ce ya matukar kaduwa bayan da masoyiyar tasa ta ce ba ta da ra'ayinsa a yanzu bayan dawowar da suka yi daga cin abincin.

Wannan lamari ya sa maudu'in #KeepTheChangeBae ke ci gaba da jawo muhawara a kafafen sada zumunta da muhawarar kasar.

Soyayyar da saurayin yake yi wa budurwarsa ta sauya salo saboda yadda ta watsa masa kasa a ido.

Lamarin ya bakanta masa rai inda ya je shafinsa na Twitter ya wallafa labarin kuma ya bayyana sunan matar a matsayin @MissMoshiku, inda ya zage ta ya kuma kira ta da "Mayunwaciya".

Ita kuwa sai ta kasa jure irin zagin da yake mata a shafinsa na Twitter, sai ta lissafa adadin dala 10 da ya kashe mata, ta kuma tura masa dala 13 a asusun ajiyarsa na banki.

Baya ga haka kuma sai ta ce masa, "ya rike sauran canjin ta bar masa."

Mutane da kamfanoni da dama sun yabe ta a kan yadda ta bullowa al'amarin.

Wani sanannen banki a Najeriya ma ya yanke shawarar zai mayar mata fiye da abin da ta saka wa saurayin a asusunsa.

Wani kamfinin sayar da gashin da mata ke karawa a kansu,nsu ya bata kyautar gashi da yake sayarwa.