Shin hana kasuwancin hauren giwa a China zai kare giwaye?

Giwaye Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farautan giwaye ba bisa ka'ida ba yasa yawan giwayen da ke Afurka ya ragu zuwa kasa da rabin miliyan

Liu Fenghai ya yi kudi sosai da kasuwancin hauren giwaye. Akwai lokacin da yake da masassaka 25 wadanda musamman suke mai aiki a kan hauren giwaye a masana'antarsa da ke arewacin Harbin.

Ya kan sayi hauren giwayen kuma ya canza su zuwa kwadon sarka da kayan adon gida da mutun-mutumi wadanda ke cika shagonsa.

A lokutan da aka fi ciniki, ana iya sayar da wasu har dala 1000.

A yanzu masu fafutukar kare muhalli da dabbobi za su yi farin ciki, China ta bukaci a dakatar da wannan kasuwanci da ke kai wa ga zubar da jinin dabbobi.

Amma Mista Liu, kamar yadda watakila za ku yi zato, ya yi matukar bakin ciki da wannan batu.

"Na yi matukar bakin ciki", a cewar mutumin mai shekara 48. "Sam bana jin dadi. Wannan abu ne da aka saba a cikin dubban shekaru amma a yanzu za a kashe shi."

Ya kara da cewa "Ji na nake kamar mai zunubi. A shekaru 100 masu zuwa, za a rika kallonmu a matsayin masu zunubi a tarihi".

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Duk da yawan kwacen hauren da ake yi a duniya, kamar wannan a Thailand, ana cigaba da fasakaurin hauren giwa

A zahiri, duk da cewa an dade ana sassakar hauren giwa a China, a mafi yawan lokuta, kasar na amfani da su a matsayin abubuwan zane-zane kuma ba ta samun ribar komai a kasuwancin.

A karni na 19 da 20, turawan mulkin mallaka ne ke kashe giwayen daga baya kuma sai 'yan kasuwar Amurka suka fara.

Bukatar da kasashen yamma ke da ita ta kayan da ake samarwa wajen amfani da haure da kananan kwallo da suke amfani da su wajen wasu wasannin ta rage yawan giwayen da ke Afirka daga sama da miliyan 20 a shekarar 1800 zuwa miliyan 2 kawai a shekarar 1960.

A shekarar 1989, lokacin da aka hana kasuwancin giwaye a duniya baki daya, shi ne giwayen suka samu saukin al'amarin.

Hakan kuma ya sauya alkibilar umarnin harkokin kudin duniya da ya jawo bala'i inda china ta kasance a matsayin daya daga cikin kasashen da suka fi karfin tattalin arziki.

A yau sakamakon, farautar namun daji da ake yi ba bisa ka'ida ba, ana kuma fuskantar karancin giwaye, inda kiyasi ke nuna cewa kasa da rabin miliyan na giwaye ne suka ragu a Afirka.

Muhimmin sauyi

A karshen wannan mako a ranar Juma'a , za a rufe dukkan masana'antun China da ake sassaka da kuma shagunan har abada.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Masu fafutuka sun ce wannan mataki da China ta dauka, wani muhimmin sauyi ne ga giwaye

Tawagar wasu jami'ai daga yarjejeniyar majalisar dinkin duniya da ke haramta cinikin dabobbin da ke barazanar karewa za su hallara don su shaidi rufewar da za a yi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matakin da china ta dauka zai iya kawo matsin lamba ka ragowar kasashen ke cigaba da kasuwancin hauren giwa kamar, Hong Kong

Za a rufe ragowar kasuwanci da kasar Chinan ke yi, wadanda suka hada da masanantu 34 da kuma shaguna 138 a bisa ka'ida zuwa karshen shekara.

Labarai masu alaka