Saudiyya ta yi wa baƙin haure afuwa

Sarki Salman na Saudiyya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A lokacin da aka dauki mataki makamancin haka an gano bakin haure miliyan 2.5

Saudiyya ta ce za ta yi afuwa ga bakin haure da dama da ke aiki a kasar idan har suka amince su bar kasar a wa'adin da ta ta dibar musu ba sai an kama su sun biya diya ko ta hukuntasu ba.

Kasar na sa ran dubban bakin hauren wadanda ba su da takardar izinin zama a kasar za su yi amfani da damar da aka ba su ta wata uku.

Kasar Saudiyya, mai arzikin man fetur, na samo ma'aikata ne daga kasashen Afirka da ma nahiyar Asiya da kuma gabas ta tsakiya.

A lokacin da aka yi afuwa makamanciyar wannan a 'yan shekarun da suka gabata, an gano cewa akwai bakin haure miliyan 2.5 a kasar.

Wakilin BBC ya ce akwai yiwuwar alkalumman sun fi haka yawa a yanzu.

Labarai masu alaka