China: An haramta tsayar da gemu a Xinjiang

Uighur
Image caption 'Yan kabilar Uighur na zaune a yankin Xinjiang

Hukumomi a yankin Xianjing na kasar China sun haramtawa musulmai 'yan kabilar Uighur tsayar da gemu da sanya hijabi.

Sauran haramcin dai sun hada da:

  • Dole ne 'ya'yan Uighur su rinka halartar makarantun gwamnati
  • Damfara dokar kayyade iyali ga 'yan kabilar
  • Gudanar da bukukuwan aure ta hanayar addinin musulunci kadai

Yankin dai ya dauki wannan mataki ne da manufar dakushe kaifin kishin addinin Islama na 'yan kabilar.

Wasu dai na ganin babu abin da haramcin zai haifar illa mayar da al'ummar saniyar ware.

Sannan kuma zai yi barazana ga al'adunsu da suka gada tun iyaye da kakanni.

Musulman dai 'yan kabilar ta Uighur sun dade suna fafitukar neman yancin kai, al'amarin da ya sanya su sanya kafar wando daya hukumomi.

Image caption 'Yan kabilar Uighur sun kai kaso 45 na yawan jama'ar Xinjiang