Gwamna Shettima ya roƙi majalisa ta mayar da Ndume

Sanata Ali Ndume Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Sanata Ndume ya ce babu gudu babu ja da baya

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Kashim Shettima, ya roki majalisar dattawan kasar ta janye dakatarwar da ta yi wa Sanata Mohammed Ali Ndume.

Gwamna Shettima, wanda ya jagoranci sarakuna da dattawan jihar domin kai ziyara ga shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki, ya ce bai kamata a dakatar da Sanata Ndume ba musamman ganin irin rawar da yake takawa wurin kawo karshen kungiyar Boko Haram da kuma wakilcin da yake yi wa jihar na gari a majalisar dokokin.

Wata majiya da ke kusa da gwamnan ta shaida wa BBC cewa, "Dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Mohammed Ali Ndume ba karamin koma-baya za ta jawo mana ba; kar ka manta kusan babu dan majalisar da ke taka rawa wurin ganin an murkushe Boko Haram kamarsa. Ndume na cikin kwamitin tarayya da ke fafutikar ganin an sake gina arewa maso gabashin Najeriya."

A cewar majiyar, gwamna Shettima ya gana da Saraki da mataimakinsa Ike Ikweremadu da 'yan majalisar dattawa daga arewacin kasar, duk dai da zummar rarrashin su su janye dakatarwar da suka yi wa Sanata Ndume.

Zarge-zarge

Majalisar dattawan dai ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjayen nata ne saboda korafin da ya gabatar mata cewa ana zargin shugaban majalisar da shigo da mota kasar ba bisa ka'ida, yayin da shi kuma Sanata Dino Melaye ake zarginsa da amfani da takardar shaidar digiri ta bogi.

An dakatar da shi ne bayan kwamitin da'a na majalisar ya wanke Bukola Saraki, da Dino Melaye daga wadannan zarge-zarge.

Kwamitin ya kuma nemi a dakatar da Sanata Ndume daga majalisar na tsawon ranakun zaman majalisar 181.

Sai dai majalisar ta rage dakatarwar zuwa wata shida.

Babu gudu babu ja da baya

Shi dai Sanata Ali Ndume ya ce ya dago batun zarge-zargen ne domin kada 'yan Najeriya su rika yi wa majalisar kallo a matsayin wani dandali na taruwar marasa gaskiya.

A cewarsa, maimakon majalisar ta yi bincike kan batutuwan da ya dago, ta kawar da su gefe guda sannan ta hukunta shi a kan laifin da bai yi ba.

Dan majalisar dattawan ya ce majalisar ta dakatar da shi ne bayan ya tafi sallar azuhur, yana mai cewa ko yanzu ya sake ganin wani abu da zai rage martabar majalisar zai gabatar da korafi a kansa.

Labarai masu alaka