An ayyana dukiyar da manyan jami'an gwamnatin Trump suka mallaka

Ivanka Trump da Jared Kushner Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ivanka Trump da Jared Kushner na da kaddarorin da suka kai $740m

Wasu takardu da fadar gwamnatin Amurka ta fitar sun nuna makudan kudin da manyan jami'an gwamnatin Donald Trump suka mallaka.

Takardun sun nuna cewa 'yar gidan shugaban kasar Ivanka da mijinta, Jared Kushner, suna da kaddarorin da suka kai tsakanin $240m da $740m.

Hakan ya hada da jarin da suke da shi a Otal-otal din Trump da ke fadin duniya, wadanda a bara suka samar wa Ivanka Trump tsakanin $1m da $5m.

Takardun sun kuma fayyace albashin da manyan jami'an gwamnatin Trump suke karba.

Dokokin kula da da'a na kasar sun bukaci a ayyana yawan kudiyar da manyan jami'an da ke aiki a fadar White House suka mallaka.

Takardun sun nuna kudi da kaddarorin da jami'an suka mallaka a lokacin da suka soma aiki da gwamnatin Amurka.

Sai dai ba su bayani kan dukiyar da Shugaba Trump da mataimakinsa Mike Pence suka mallaka ba.

Ga wasu daga cikin jami'an gwamnatin da kuma dukiyarsu:

  • Ivanka Trump tana gudanar da harkokin kasuwancin da suka wuce $50m, sannan tana da jari a Otal-otal din mahaifinta da ya kai tsakanin $5m da $25m
  • Jared Kushner, mijin Ivanka yana rike da mukamai a kamfanoni 267, kodayake ya janye hannunsa daga cikin da dama. A bara, ya samu dubban daloli daga harkokin gine-gine da wasu harkokin.
  • Steve Bannon, wanda shi ne bban jami'in da ke bayar da shawara a fadar White House, ya samu $191,000 a matsayin kudin tuntuba na aikin da ya yi wa kafar watsa labarai mai tsattsauran ra'ayi, Breitbart, baya ga $1m da ya samu daga wasu ayyukan da ya yi. Yana kuma da kaddarorin da suka kai tsakanin $3.3m zuwa $12.6m.
  • Sean Spicer, mai magana da yawun fadar White House ne, kuma an biya shi $260,000 a matsayinsa na babban mai tsare-tsare da sadarwa a kwamitin yakin zaben jam'iyyar Republican, sannan yana da kaddarori da dama.
  • Kellyanne Conway, ita ce babbar jami'ar yakin neman zaben Trump wacce ta zama mai ba shi shawara, kuma tana da $800,000, kafin ta soma aiki a fadar White House. Ta samu yawancin kudinta ne daga ayyukan tuntuba da ta yi, ciki har da jagorancin yakin neman zaben Trump.
  • Gary Cohn, shi ne shugaban majalisar kula da tattalin arziki ta fadar White House kuma tsohon shugaban bankin Goldman Sach, wanda ke da kaddarorin da suka kai $230m - ko fiye da haka.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kiyasta cewa jami'an gwamnatin Donald Trump sun mallaki $12bn

Labarai masu alaka

Karin bayani