Zaftarewar ƙasa ta yi sanadin mutuwar mutane da dama a Indonesia

Java mudslide, 1 April Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaftarewar ƙasar ta lalata gida 30

Akalla mutum 11 ne ake fargabar sun mutu bayan zaftarewar da ƙasa ta yi sakamakon ruwan sama kamar da bakin-ƙwarya da aka sheƙa a lardin Java na ƙasar Indonesia.

Zaftarewar ƙasar ta faru ne a ƙauyen Banaran da ke gundumar Ponorogo da safiyar ranar Asabar, inda ta lalata gida 30, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar.

Jami'an tsaro da na bayar da agajin gaggawa na ci gaba da kawar da lakar da ta danne mutane domin fitar da su.

Ana ci gaba da kwashe mutane daga yankin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da mutane ke cirar citta daga gonakinsu, in ji jami'an yankin.

Ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa abubuwa ne da aka saba yi a Indosenia musamman a lokutan damuna.

Mutane da dama a tsuburan kasar 17,000 na zaune ne a yankuna da ke da duwatsu ko kuma wuraren da ke da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa.

Labarai masu alaka

Karin bayani