Sojoji sun kama masu yi wa Boko Haram leƙen asiri

Sojojin Najeriya sun gargadi mutane kan 'yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sojojin Najeriya sun gargadi mutane kan 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami'anta sun kama wasu mutane da ke yi wa kungiyar boko Haram leken asiri.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman ya aike wa manema labarai ta ce dakarunsu da ke Bataliya ta biyar ne suka kama mutanen ne a kauyen Kareto da Dangalti da ke jihar Borno.

Birgediya Janar Kukasheka ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa mutanen suna yin leken asiri a kauyukan ne da zummar kaddamar da hari a kansu daga baya ba tare da wata matsala ba.

Kakakin rundunar sojin ta Najeriya ya kara da cewa dakarunsu sun kama wasu daga cikin kwamandojin Boko Haram.

A cewarsa, "An kama Bulama Kailani Mohammed Metele daga Tumbun Bera, wanda ya amince cewa shi dan Boko Haram bangaren Mamman Nur. Kuma da alama ya mika wuya ne ga dakarun runduna ta 145 da ke Damasak saboda ya gaji da karairayin da shugabanninsu ke yi masa."

Birgediya Janar Kukasheka ya ce sun tabbatar cewa Bulama Kailani Mohammed Metel, babban dakaren kungiyar Boko Haram ne, yana mai cewa yana cikin 'yan kungiyar da rundunar sojin Najeriya ke nema ruwa a jallo.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Boko Haram ta koma kai harin sari-ka-noke

Sojojin na Najeriya dai sun ce sun ci karfin mayakan kungiyar ta Boko Haram, ko da yake sun sha yin kira ga 'yan kasar da su rika sanya idanu kan abubuwan da ke wakana a inda suke domin kaucewa masu yin kunar-bakin-wake.

Labarai masu alaka