Niger ta ƙaddamar da tashar samar da lantarki a Gorou Banda

Jamhuriyar Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karancin wutar lantarki ya addabi jama'a a jamhuriyar Nijar

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ƙaddamar da wata tashar samar da lantarki a Gorou Banda, mai karfin megawat 80, don shawo kan ƙarancin wutar da ake fama da ita musammam a yankin birnin Niamey.

Shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou ne ya ƙaddamar da tashar a ranar Lahadi, don bunƙasa lantarkin da ake samarwa ga al`ummar Yamai, babban birnin kasar.

Yawan ɗauke wutar lantarki matsala ce da ta jefa jama'ar birnin Yamai da dama cikin wawuyacin hali.

Galibi dai yanzu sun fi dogaro da injinan janareta don samun hasken lantarki da kuma gudanar da sana'oi'n da suka danganci amfani da lantarkin.

Wani magidanci ya shaida wa BBC cewa kwanan nan ba sa samun wuta sosai, sun shiga wani hali, sukan kunna janareta da rana don su samu saukin zafin da ya addabe su.

''Rashin wutar lantarki na kawo mana matsaloli da yawa, ga yanayin zafi, kaya ba su ajiyuwa suna lalacewa.''

Mai Shero Bala Mamman jami'i ne a cibiyar samar da wutar lantarkin ta Gorou Banda kuma ya ce nan gaba idan tafiya ta yi nisa, za a ƙara samun wutar da ta kai ƙrfin megawat 150 .

''Megawat 80 ba zai isa ba, dole sai an ƙara ƙarfin lantarkin matuƙar ana son shawo kan wannan matsala, in ji shi.''

Ya kuma ce ana gudanar da aiki kan samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana ta yadda matsalolin da ake fama da su na rashin wutar za su ragu.

Matsalar karancin wutar lantarki kusan ta zama ruwan dare a akasarin kasashen Afirka.

Labarai masu alaka