Da wuya a samu ƙarin mai rai a zaftarewar lakar Colombia

Birnin Mocoa na kasar Colombia Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Akasarin wadanda suka mutu a zaftarewar kasar kananan yara ne

Wasu rahotanni a kasar Colombia na cewa babu alamun samun sauran masu rai a ɓaraguzan gine-gine da laka ta yi ambaliya da su tun ranar Juma'a a birnin Mocoa.

Daruruwan sojojin Colombia da ma'aikatan agaji sun shiga aikin ceto a birnin da ke kudancin ƙasar, don zakulo mutanen da zaftarewar laka ta rufe.

Kimanin mutum 300 ne aka ba da rahoton ɓatansu, baya ga wasu 250 da suka mutu kuma fiye da arba'in a acikinsu ƙnanan yara.

Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos -- da ke ziyara a Mocoa ya ce za su gyara birnin.

Mamakon ruwan sama ne ya haifar da ambaliya a birnin Mocoa da ke kudu maso yammacin Colombia, inda tabo da duwatsu suka yi awon gaba da ɗaukacin yankin, abin da ya tilasata wa mutane tserewa.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce tana gudanar da aikin sada iyalai da 'yan'uwansu, yayin da sojojin saman Colombia ke jigilar kayan agaji.

Wata mata ta koka kan faruwar lamarin a lokacin da take fatan ganawa da 'ya'yanta da suka ɓace.

'' Ina neman yayana mata biyu, da kuma jikata, ko a mace ko a raye, ni dai ina so in gan su.''

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Image
Image caption Zaftarewar kasar ta yi ta awon gaba da ababan hawa

Zai dai yi matukar wahala a iya tabbatar da ainihin adadin wadanda suka mutu, yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin ceto.

Wasu kafafen yada labaran yankin dai sun kididdige cewa mutane kusam 300 ne suka mutu, yayin da kungiyar ba da agaji ta Red Cross ke cewa sun haura 200.

Wata kwararriya a fannin kimiyyar halittu daga jami'ar El Rosario a birnin Bagota, Carolina Pardo ta shaida wa BBC cewa rashin alkinta muhalli, da sare itatuwa na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da zaftarewar kasar.

'' Akasarin mutane a Mocoa na gina gidaje a bakin kogi, ba ma a Macoa kadai ba, har ma da sauran yakunan da ke kewaye.''

''Mutane na gida gidaje, da gonakinsu a kusa da koguna, kuma suna sare itatuwa da tsirrai, don haka babu wata jijiya da za ta rika kare ƙasa a kusa da kogunan.''

A cikin watan Nuwamba, mutane 9 ne suka mutu a El Tambo mai nisan kilomita 140 daga birnin Mocoa, lokacin wata zaftraewar kasar ta auku sakamakon wani ruwan saman da aka tafka.

Kasa da wata guda kafin nan, wata zaftarewar kasar ta hallaka gomman mutane a kusa da Medellin, mai nisan kilomita 500 daga arewaci.

Labarai masu alaka