Za a fuskanci wahalar man fetur a Nigeria — NUPENG

NUPENG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar NUPENG ta ce lalatattun titunan Najeriya suna bata musu motocin daukar mai

A ranar Litinin ce direbobin manyan motocin dakon man fetur za su fara yajin aiki a Najeriya.

Kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG, ta ce za tu shiga yajin aikin ne saboda karancin albashi da lalatattun titunan kasar da suke bata musu motoci.

Wani mai magana da yawun kungiyar Cogent Ojobo, ya yi gargadin cewa za a fuskanci wahalar karancin man fetur da dizal da kananzir a kasar, saboda za su dakatar da rarraba su.

Ya kuma ce ba a saka ranar da ake zaton daina yajin aikin ba.

Hakan na nufin tattaunawar da aka yi tsakanin NUPENG da gwamnatin tarayyar Najeriya bai yi tasirin hana kungiyar shiga yajin aikin ba.

Wannan ba shi ne karo na farko da kungiyoyin kwadagon ma'aikatan man fetur ke shiga yajin aiki ba a Najeriya, kuma a duk lokacin da suka shiga to ana fuskantar matukar wahalar man a kasar.

Tun a ranar Asabar hankalin 'yan kasar ya fara tashi sakamakon rade-radin yajin aikin da suka ji, inda gidajen mai suka fara cika da motoci.

Mutane sun ta cika tankunan motocinsu da mai, har ma suna saye a jarkoki duk saboda tanadi don tsoron fuskantar wahalar karancin man.

Labarai masu alaka