Kauyen da yara ke rayuwa ba tare da iyayensu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shin kun san ƙauyen da yara ke rayuwa ba tare da iyayensu ba

Rabin 'ya'yan da ke wani ƙauye a Indonesiya suna tasowa ne ba tare da iyayensu ba, saboda iyayen na barin su su tafi wasu ƙasashen don neman aikin da za su rufawa kansu asiri.

Don sanin halin da wadannan yara ke ciki, BBC ta ziyarci gundumar gabashin Lombok, inda nan ne aka fi saninsu da tafiya ci rani wasu ƙasashen.