'Yan fashi sun kwace jirgin ruwan Indiya a Somaliya

A Somali pirate keeping vigil near Hobyo, in Somalia - Archive shot Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu raguwar yin fashi a gabar tekun Somaliya a shekarun baya-bayan nan

Jami'ai sun bayyana cewa 'yan fashin teku a kasar Somaliya sun kwace jirgin ruwan dakon kaya na Indiya a gabar tekun yankin Puntland mai kwarya-kwaryar cin gashin kai.

Wata majiya ta ce, jirgin na kan hanyarsa ta zuwa gabar tekun Somaliya ne. Babu wani cikakken bayani kan inda ma'aikatan jirgin suke a yanzu ko kuma inda aka karkata akalar jirgin.

Makonni biyu da suka gabata ma wasu 'yan fashi teku sun kwace jirgin ruwan dakon mai a kan hanyarsa ta zuwa garin Mogadishu, daga bisani suka saki jirgin ruwan ba tare da wani sharadi ba.

Wannan ne fashin jirgin ruwa na farko da aka yi a gabar tekun Somaliya tun shekarar 2012.

Tsohon Daraktan hukumar yaki da masu fashin teku na yankin Puntland, Abdirizak Mohamed Dirir, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, "Mun fahimci cewa masu fashin teku na kasar Somaliya sun yi wa jirgin ruwan'yan kasuwa na kasar Indiya fashi a kan hanyarsa ta zuwa gabar Somaliya".

Shafin Intanet na kamfanin Daynile ya ce harin ya faru ne kusan kilomita 50 daga kudancin garin Hobyo.

Fashin da ake yi a gabar tekun Somaliya wanda yawanci ana yin sa ne don karbar kudin fansa ya ragu sosai a kasar a shekarun baya-bayan nan, saboda yawaita sintirin da sojojin da kasa-kasa ke yi da kuma goyon bayan da ake samu daga wurin kananan kungiyoyin masu kamun kifi.

A lokacin da ake cikin tsananin fuskantar wannan matsala a shekarar 2011, an kai hari sau 237 kuma an yi fashin kudin da ya kai kimanin dala biliyan takwas a cikin shekara daya.

Labarai masu alaka

Karin bayani