Amurka kadai za ta iya maganin Koriya ta Arewa — Trump

This combination of pictures created on March 30, 2017 shows China's President Xi Jinping (L) delivering a speech on the opening day of the World Economic Forum, on January 17, 2017 in Davos, and US President Donald Trump (R) announcing the final approval of the XL Pipeline in the Oval Office of the White House on March 24, 2017 in Washington, DC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mista Trump zai gana da shugaba Xi Jinping ranar Alhamis

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kasarsa za ta yi maganin Koriya ta Arewa kan batun makamin nukiliyarta, ko da taimakon China, ko babu.

A wata hira da yayi da wata Jaridar Burtaniya mai suna Financial Times, shugaban ya ce, "Idan China ba za ta magance matsalar Koriya ta Arewa ba, to mu za mu iya, wannan shi ne abin da nake gaya muku."

Da aka tambaye shi ko yana ganin cewa zai iya yin nasara shi kadai, sai ya ce "Sosai ma."

Mista Trump yana magana ne gabannin ziyarar da shugaban China Xi Jinping zai kai masa a wannan makon.

Mista Trump ya ce, "China na da karfin fada aji kan Koriya ta Arewa. Don haka ko dai China ta taimaka mana mu yi maganin Koriya ta Arewa ko kuma ta yanke shawarar kin yin hakan. Idan ta taimaka din to ta yi abin da ya dace, idan kuwa ta ki taimakawa to abin ba zai yi wa kowa dadi ba."

Da aka tambaye shi ko yana nufin Amurka za ta iya fito-na-fito da Koriya ta Arewa ita kadai, sai ya ce, "Ba na bukatar yin dogon bayani."

Bai dai yi karin bayani ba game da matakin da zai dauka.

Me ya shafi Amurka da wannan matsalar?

Wadannan maganganu da aka wallafa kwanaki kadan kafin saduwar Mista Trump da Mista Xi a Florida ranar Ahhamis, su ne na baya-bayan nan a jerin gargadin da Amurka ke yi wa Koriya ta Arewa kan makamin nukiliyarta.

Akwai dai fargaba game da cewa Koriyar za ta kai matakin kera makami mai nisan zango wanda zai iya kai wa ga kasar Amurka.

Hakkin mallakar hoto Twitter/@realDonaldTrump

Me ce ce mafita?

A ziyararsa zuwa nahiyar Asiya a watan Maris, Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ya ce amfani da karfin Soji ma hanya ce ta tsayar da Koriyar daga aniyarta.

Wata guda kafin nan sakataren Tsaron Amurka James Mattis, ya yi gargadin cewa duk wani shiri na amfani da makaman kare-dangi zai hadu da karfin Soji.

Sai dai kuma an yi amanna cewar amfani da karfin soji kan Koriya ta Arewa zai haifar da jikkatuwar fararen hula da sojoji.

Jami'an Amurka sun ce tsarin amfani da karfin soji kan Koriya, abu ne da aka tattauna shekaru masu yawa da suka gabata, amma an yi ta amfani da takunkumi, da hanyoyin diflomasiyya kan Koriyar ko za ta tsayar da shirin nata.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma kasashe da dama sun sanya wa Koriyar takunkumi da kuma kawo cikas ga karfin tattalin arzikinta a kasahen waje, domin ta tsaida shirin nata.

Haka kuma taimakon abinci da ake bai wa Koriyar, wacce ta dogara da taimakon domin ciyar da mutanenta, ya ragu a 'yan shekarunnan.

Sai dai wannan matakin bai ragewa kasar karfi ba ta bangaren karfin Soji.

Ana ganin cewar sanya takunkumin da zai shafi masu shiga tsakani, wadanda ke barin Koriyar na ci gaba da shirin nata, kamar bankunan China, zai taimaka sosai, kamar dakatar da shigar da mai da Koriyar take yi daga China.

Shin Amurka za ta iya ita kadai? Sharhin wakilin BBC kan tsaro da diflomasiyyia, Jonathan Marcus:

Koriya ta Arewa ta zama kasa ta farko da gwamnatin Trump za ta sanya wa dokar soji, sai dai matsalar Amurkan ba za ta iya ita kadai ba. China na da matukar amfani a lamarin.

Shugaba Trump dai ya nanata cewa zai iya dakile shirin Nukiliyar Koriya ta Arewa shi kadai a wannan gaba da ake tattaunawa tsakanin kasashen Amurka da Rasha.

Hakika hukumar tsaro ta Amurka na da shirin amfani da karfin Soji kan kasar Koriya, wasu masu dadi, wasu marasa dadi.

To sai dai duk wani shiri na Amurkan domin Koriyar ta tsayar da shirin nata ba mai yiwuwa ba ne, saboda Koriya ta Arewa za ta lalata babban birnin Koriya ta kudu wato Seoul, da manyan makaman Atilari, da rokokin yaki, don haka duk wani yunkurin Amurka ba zai samu nasara ba.

Har yanzu dai ana mayar da hankali ne kan ganin Koriyar ta tsaida shirin nata na Nukiliya. Har yanzu ba ta nuna alamarza ta yi hakan ba. Amma har yanzu China tana da rawar da za ta taka.

Batun Kasuwanci

Ana sa ran Mista Trump zai matsa wa shugaban China lamba a kan Koriya ta Arewa a tattaunawar da za su yi a wannan makon. Kuma ya nuna cewa batun kasuwanci wani abu ne da za a yi amfani da shi.

Trump ya fada wa Jaridar Financial Times cewa, "Kasuwanci ma wani abu ne," sai dai ya ce bai shirya tattaunawa da shi ba a kan batun haraji a yayin ziyarar.

A karshen watan Maris, ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi biyu da za su taimaka wa kasuwancin Amurka, yayin sake duba sabbin dokokin kasuwanci kasashen waje.

Masu sharyi dai na ganin cewa China za ta ci gaba nuna goyon bayanta ga Koriyar, saboda ta san faduwar kasar zai sa ta hade da Koriya ta kudu, wacce ke samun goyon bayan sojojin Amurka da ke da iko da iyakar kasar da China.

Saboda haka ana ganin cewa Chinan ce za ta dauki miliyoyin 'yan gudun hijirar da za su tsallake kan iyaka.

Labarai masu alaka

Karin bayani