Nigeria: Buhari ya yi ganawar sirri da Dogara da Saraki

Dangantaka tsakanin bangaren shugaban Buhari da kuma majalisar dokokin Najeriya na dada kamari Hakkin mallakar hoto Nigeria Government

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da Kakakin majalisar wakilan kasar Yakubu Dogara da kuma shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a lokuta daban-daban cikin sirri.

Mista Dogara ne ya fara isa fadar gwamnatin kasar da ke Abuja da misalin karfe 12 inda nan take ya shiga domin ganawa da shugaban.

Shi kuwa Bukola Saraki ya isa ne minti 30 bayan isowar Dogara, sannan ya fara ganawa da shugaban bayan tafiyar Dogaran.

Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da takun-saka tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ke kara ta'azzara.

Babu tabbacin dalilin da ya sa shugabannin majalisar dokokin kasar ba su gana da shugaban kasar tare ba, kuma babu bayani kan abin da suka tattauna.

Amma ba zai rasa nasaba da takun-sakar da ake yi tsakanin bangaren zartarwa da na dokokin kasar ba.

Takun-sakar dai ta kai har majalisar dattawan kasar ta dakatar da tantance mutanen da shugaban ya nada kwamishinoni a hukumar zaben kasar.

Majalisar dattawan ta ce ta dauki matakin ne saboda shugaban kasar bai dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci ta (EFCC) Ibrahim Magu ba, duk da cewa majalisar ta ki ta tabbatar da shi.

Labarai masu alaka