'Riga-kafin sankarau ya yi wa Najeriya tsada'

. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption $50 ne farashin kowacce allurar riga-kafin sankarau

Hukumomi a Najeriya sun ce ba za su iya sayen allurar riga-kafin sankarau din da ke addabar al'umma a kan naira dubu 15 kowacce ƙwaya ɗaya ba.

A wata hira da ya yi da sashen Ingilishi na BBC, shugaban hukumar hana bazuwar cututtuka, Chike Ihekweazu, ya ce maimakon kasar ta sayi allurar riga-kafin kan naira 15000 wato $50, akwai bukatar a duniya a kara yawan allurar rigakafin da ake sarrafawa na wannan nau'in cutar sankarau din da ake fama da ita domin a karya farashinta.

Sai dai shugaban ya kara da cewar gwamnatin Najeriya za ta yi iya kokarinta domin ta samar da isasshiyar allurar riga-kafin domin hana ci gaba da yaduwar cutar a kasar.

Kawo yanzu kimanin mutum 320 ne jami'ai suka tabbatar cutar ta kashe tun bayan bullarta a kasar.

Mista Ihekweazu ya ce hukumar za ta fara bayar da allurar riga-kafin ne a fadin Najeriya ranar Juma'a mai zuwa, 7 ga watan Afrilu.

Ya kara da cewa bayan gudanar da riga-kafin, hukumar za ta gabatar da korafi ga duniya don nuna cewar bai dace a sayar da allurar riga-kafin kan dala 50 ba, a lokacin da cutar ta ke yaduwa a Najeriya da kuma wasu wurare a Afirka ta yamma.

Labarai masu alaka