Juventus za ta dauki Rodrigo Bentancur a matsayin musanyar Tevez

Rodrigo Bentancur Hakkin mallakar hoto BBC Sport
Image caption Rodrigo Bentancur ya taimaka wa kasar Uruguay daukar kofin matasa na kudancin Amurka na 2017.

Dan wasan tsakiya na Boca Juniors, Rodrigo Bentancur na Juventus domin gwajin lafiya.

Rodrigo Bentancur ya taimaka wa kasar Uruguay daukar kofin matasa na kudancin Amurka na 2017.

Zakarun na Italiya suna dab da daukar matashin dan wasan, watau Rodrigo Bentancur daga kungiyar Boca Juniors.

Bentancur, mai shekara 19, ya isa birnin Turin ranar Litinin domin yin gwajin lafiyarsa kafin ya hade da Zakarun na Serie A.

Dan wasan kasa da kasar na Uruguay wanda ke cikin tawagar kasar ta 'yan kasa da shekara 20, na murza leda ne a kungiyar matasan Boca Juniors dake kasar Argentina.

Juventus ta kulla yarjejeniyar sayen dan wasan ne, lokacin da dan wasan gabanta Carlos Tevez ya koma Boca Juniors, daga Juventus a watan yunin 2015.

Juventus din dai na mataki na daya a gasar Serie A, da ratar maki shida, yayin da ya rage wasanni takwas a kammala gasar, a kokarinsu na daukar kofin sau shida a jere.

Haka kuma kungiyar da Massimiliano Allegri ke wa Koci ta kai wasan dab da kusa da karshe a gasar kofin zakarun Turai, inda za ta kara da Barcelona har sau biyu a ranakun 11 da 19 ga watan Afrilu.

Labarai masu alaka