Trump na goyon bayan Sisi dari bisa dari

Shugaba Donald Trump da Shugaba Abdul Fattah al-sisi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce an kama dubun dubatar mutane a lokacin juyin juya halin da aka yi a Masar

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce, yana goyon bayan Mista Sisi, wanda gwamantin Obama ya soki matakansa dari bisa dari.

Mista Sisi ya bayyana godiya ga irin "halayen Trump da yasa ya yi fice".

Jami'an Amurka sun ce Mista Trump naso ya "farfado" da dangantaka a wurin tattaunawar da shugabannin biyu za su yi.

Mista Trump yana kuma so ya karfafa alakar da ya kulla da Mista Sisi a watan Satumban bara, a lokacin da yake yakin neman zabe a birnin New York.

A lokacin da yake a matsayin ministan tsaro a watan Yulin shekarar 2013, Mista Sisi ne ya shugabanci juyin juya halin da ya kai ga hambarar da shugaban da aka zaba na farko, Mohammed Morsi , bayan an yi zanga-zangar kyamar shugabancin sa.

Wata guda bayan haka, ya fuskanci zanga-zanga mai cike da tashin hankali daga wurin magoya bayan Mista Morsi da 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi, wanda yayi sanadiyar mutuwar sama da mutum 1,000.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce an kama dubun dubatar mutane a lokacin kuma jami'an tsaro sun aikata munanan laifuka wadanda suka hada da cin zarafi da kisa ba tare an yankewa mutum hukuncin kisa ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Sisi ya fuskanci zanga-zanga mai cike da tashin hankali daga wurin magoya bayan Mista Morsi

Mista Sisin wanda aka zaba a watan Mayun shekarar 2014, ya kuma saka takunkumi kan damar da 'yan kasar ke da ita a matsayinsu na dan adam da kuma ta siyasa, wanda a cewar kungiyar ya kawar da alfanun rikcin da yayi sanadiyar kifar da gwamnatin Hosni Mubarak.

Barack Obama ya dakatar taimakon da Amurka ke bai wa Masar a matsayin wani martani na juyin juya halin Oktobar 2013.

Ya kuma dage kan cewa takunkumin zai dore ne har sai Masar ta bayyana alamun cigaba ta fannin demokuradiyya, amma kuma sai ya cigaba da bai wa sojin kasar taimaka a watan Afrilun shekarar 2015 saboda kare tsaron Amurka.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarar 2013 ne dai Barack Obama ya dakatar taimakon da Amurka ke bai wa Masar

Wani babban jami'i a gwamnatin Trump ya shaidawa manema labarai cewa za a tattauna kan damuwar da kungiyar kare hakkin dan adam ke da ita a ganawar da za a yi ranar Litini, amma za yi hakan ne cikin sirri.

Tun shekarar 2013, kungiyar masu fafutukar Islama dake zaune a yankin Sinai sun kashe daruruwan jami'an tsaron Masar.

An yi amannar Mista Sisi na son ya samu kari kudin a kan dala biliyan 1.3 na tallafin da Amurka ke bai wa sojojinta wajen yakar kungiyar IS.

Labarai masu alaka