Kun san wanda ya kai harin jirgin kasa a Russia?

Kasar Russia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutumin da ya kai harin St Petersburg dan yankin tsakiyar Asiya ne

Hukumomi a birnin St Petersburg na Rasha sun ce mutane 41 ne ke can a asibiti suna karɓar magani bayan fashewar wani abu a cikin jirgin ƙasa ranar Litinin.

Mutum 11 ne aka ba da sanarwar mutuwarsu sakamakon fashewar wadda masu shigar da ƙara ke ɗauka a matsayin aikin 'yan ta'adda ne.

Kafofin yaɗa labarai na ambato majiyoyin tsaro da ke cewa mai yiwuwa wani ɗan harin ƙunar baƙin wake da ƙila ya fito daga tsakiyar Asiya ya tarwatsa kansa.

An kunce ƙarin wani abin fashewa na biyu da aka gano a wani wajen daban, yayin da Shugaba Vladmir Putin ke cewa hukumomin ƙasar na ƙoƙarin tabbatar da abin da ya faru.

Mutumin da ake zargi da hallaka mutane 11 a cikin jirgin kasar St Petersburg mai kimanin shekaru 20 ne, kuma dan yankin tsakiyar Asiya ne kamar yadda rahoton kafar yada labaran kasar Rasha ta bayyana.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Image
Image caption An kuma gano wani abin fashewar a kusa da inda aka kai harin na St Petersburg

Mahukunta a birnin na St Petersburg sun ayyana zaman makokin kwanaki uku ga wadanda harin ya shafa.

Shugaba Vladimir Putin, da ke birnin a lokacin da harin ya faru, ya ziyarci wurin da yamamcin Litinin inda ya aza furannin juyayi a daidai wurin da aka kai harin.

Natalya Kirillova na cikin taragon jirgin da harin ya faru.

"A lokacin na ji wata gagarumar kara, mai razanarwa. Ina zaune a kusa da wasu jerin karafuna, ina ga su ne suka tserar da ni.''

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Vladimir Putin na aza furanni a daidai wurin da aka kai harin

Masu gudanar da bincike na kasar Rasha sun bayyana lamarin a matsayin harin ta'addanci, ko da yake sun bayar da takaitattun bayanai ne.

Babu dai wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kaddamar da harin.

Shugabannin kasashen duniya sun taya kasar Rasha alhini da yin Allah wadai da harin.

A wata hira ta wayar tarho, shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa Vladmir Putin cikakken goyon bayan gwamnatinsa wajen zaƙulo waɗanda ke da alhakin kai harin.