An yi girgizar kasa mai karfi a Botswana

Botswana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Har yanzu gwamnatin Botswana ba ta bayar da rahoton mutuwa ko jikkata ba

A ranar Litinin da yamma ne aka yi wata girgizar kasa mai tsananin karfi a wani surkukin yanki a kasar Botswana, kusa da wani gandun daji na Kalahari, al'amarin da ya matukar girgiza al'umma yankin.

Gwamnatin Botswana dai ta ce ba ta samu rahotannin jikkata ko mutuwa ba.

Hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar na da girman maki 6.5, kuma ta faru ne kilomita 250 daga arewa zuwa arewa maso yammacin babban birnin kasar, Gaborone.

Ta kara da cewa zurfin girgizar kasar ya kai tsawon kilomita 12.

Haka kuma, an ji motsin kasa a kasar Afrika Ta Kudu da ke makwabta da Botswanan.

Wani babban mai magana da yawun gwamnatin Botswana Jeff Ramsay, ya ce, "Hakika mun ji alamun girgizar kasar a nan babban birni na Gaborone. Gine-gine sun motsa sosai."

Ya kara da cewa, "Zuwa yanzu dai ba mu samu rahoton mutuwa ko jikkata ba, amma ya yi wuri mu fadi wani abu a kan hakan."

Wani basarake na wani kauye kusa da wajen da abin ya faru, Kgosi Kgomokgwana, ya ce, "Wannan ne karo na farko da wani abu makamancin haka ya faru a yankin nan."

Labarai masu alaka