Rikicin Syria: Harin guba ya hallaka mutane da dama

A Syrian child receives treatment following a suspected chemical attack in Khan Sheikhoun, Idlib province, Syria (4 April 2017) Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu aikin ceto sun ce yara da dama sun mutu a harin

Wata kungiyar sa ido ta ce, a kalla mutum 58 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata a wani al'amari da ya faru da ake zaton harin guba ne aka kai wani gari da ke karkashin ikon 'yan tawaye a arewa maso yammacin Syria.

Hukumar sa ido kan kar hakkin dan adam ta Syria ta bayar da rahoton cewa, hare-haren saman da jiragen yakin gwamnatin Syria suka kai Khan Sheikhoun, ya jawo numfashin mutane da dama ya yi ta shakewa.

Masu fafutuka na kasar da kafofin yada labarai sun yi ta wallafa hotunan mutanen da aka ce sun mutu sakamakon shakar gubar da suka yi.

Gwamnatin Syria dai ta sha musanta cewa tana amfani da makamai masu guba.

An tabbatar da cewa wannan hari shi ne harin guba ma fi muni da aka taba kai wa Syria tun lkacin da aka fara yakin basasar kasar shekara shida da ta gabata.

Wani dan agaji mai aiki da motar daukar marasa lafiya a Idlib, Mohammed Rasoul, ya shaida wa BBC cewa ya samu labarin hare-haren saman ne da misalin karfe 3.45 na tsakar daren Litinin agogon GMT.

A lokacin da motar tasa ta isa wajen da abin ya faru, ma'aikatan jinya sun ga mutane na ta gwagwarmayar shakar numfashi.

"Har yanzu tawagarmu tana nan, muna kara-kainar kai mutane daga nan zuwa can, saboda asibitoci sun cika," in ji shi.

Ya kara da cewa, "Ina magana da abokan aikina kuma suna lafiya, amma dai halin da ake ciki a wajen ba dadi, kuma ma fi yawan wadanda suke shan wahala yara ne."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu an kasa gane wane irin sinadari a ka yi amfani da shi

Mista Rasoul ya bayar da rahoton cewa, mutum 67 ne suka mutu, 300 kuma suka jikkata, yayin da wata kafar yada labari da ke goyon bayan bangaren adawar kasar kuma ta ce, mutum 100 ne suka mutu.

Hukumar sa ido kan kar hakkin dan adam ta Syria ta bayar da bayaninta kan abin da majiyoyin lafiya suka fada, inda aka ce yara 11 na daga cikin wadanda suka mutu a Khan Sheikhoun, kuma cikin alamun da suka nuna na mutuwa sun hada da sume da amai da kuma fitar da kumfa ta baki.

Cibiyar lafiya mai goyon bayan bangaren adawa a Idlib ta wallafa hotuna da dama na mutane yayin da suke karbar agaji, da kuma hotunan wasu yara kusan bakwai a bayan wata mota a-kori-kura. Sai dai ba tabbas kan sahihancin hotunan.

Hukumar sa ido kan kar hakkin dan adam ta Syria ta ce ta kasa gano sinadarin da aka jeho wanda ya jawo wannan lamari, sai dai ana ganin wani sinadari ne mai guba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hukumar kare hakkin dan adam ta Syria ta bukaci MDD ta kaddamar da bincike

Yankin Idlib inda aka kai hare-haren na karkashin ikon 'yan tawaye ne.

Dama dai gwamnatin kasar da kawarata Rasha suna yawan kai hare-haren sama yankin, haka ma gamayyar kawancen soji da Amurka ke jagoranta na kai nata hare-haren kan 'yna kungiyar IS.

Gamayyar kawancen da ke adawa da gwamnati ta zargi gwamnatin shugaba Assad da jawo wannan mummunan hari a Khan Sheikhoun, ta kuma yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya kaddamar da binciken gaggawa kan lamarin.

A sanarwa da ta fitar, gamayyar kawancen ta ce, "Rashin yin hakan zai zama tamkar kwamitin na jin dadin abin da gwamnatin Assad ke yi ne."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane sun ta samun matsalar shakar numfashi

A shekarar 2013, kasashen yamma sun zargi gwamnatin Syria da harba rokoki masu dauke da sinadarin guba zuwa wasu yankuna da ke karkashin ikon 'yan tawaye a Damascus, babban birnin kasar, inda mutum 300 suka mutu.

Mista Assad ya yi watsi da tuhumar, amma kuma ya ki ya lalata rumbun makamai masu guba da yake da su.

Duk da haka, hukumar da ke haramta amfani da makamai masu guba ta ci gaba da tattara bayanai kan cewa Syria na ci gaba da kai hare-hare da sinadarai masu guba.

Labarai masu alaka