Ndume ne gatanmu a majalisa — Masu zanga-zanga

Ndume
Image caption Ndume ya ce yana sallah aka aika cewa an dakatar da shi

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka taru a gaban shiga majalisar dokokin Najeriya, da ke babban birnin kasar Abuja, a ranar Talata, inda suke neman a janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan kasar ta dakatar da Sanata Ndume har tsawon wata shida, saboda korafin da ya gabatar kan shugaban majalisar da kuma Sanata Dino Melaye da ke wakiltar jihar Kogi.

Tun da sanyin safiya ne masu zanga-zangar suka yi dirar mikiya a gaban majalisar dokokin, rike da takardu da aka yi rubuce-rubuce a kai, masu yin Allah-wadai da shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki.

Cikin rubutun akwai wanda ke cewa, "Saraki annoba ne."

Wasu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar 'yan gudun hijira ne daga yankin Borno ta Kudu inda Sanata Muhammad Ali Ndume ke wakilta.

Sun ce wata shiddan da aka dakatar da Ali Ndume zai hana mutanen yankin samun wakilci na gari a wurin kasafin kudi da kuma wurin zartar da dokar da ta kafa hukumar raya yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Masu zanga-zangar sun kara da cea yara da mata na kananan hukumomi tara da ke yankin Kudancin Borno, wadanda suke cikin tsanani sakamakon rikicin Boko Haram, za su rasa wakilci na rabin shekara idan majalisar ba ta janye dakatar da Sanata Ali Ndume ba.

Sanata Binta Masi Garba da ke wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya, ita ta karbi masu zanga-zangar a kofar shiga majalisar dokokin, a madadin majalisar dattawan.

Ta tabbatar wa da masu zanga-zangar cewa za ta isar da kokensu ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, domin a samu mafita a lamarin.

"Mun ji kokenku, aikinmu shi ne mu koma ga majalisar dattawa, musamman ma shugaban majalisar mu nuna masa zakuwarku da kuma kiran da ku ka yi na son a janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Muhammad Ali Ndume," in ji ta.

Sanata Ndume dai ya bukaci a binciki Sanata Saraki ne kan zargin shigo da mota da ya yi kasar ba bisa ka'ida ba da Sanata Dino Melaye kan zargin sa da amfani da takardar shaidar digiri na bogi.

Dakatar da shi din da aka yi na nufinba zai sake shiga majalisar ba, kuma ba za a biya shi dukkan alawus din da ya saba karba ba.

Labarai masu alaka