South Africa: Matsin lamba na karuwa kan Shugaba Jacob Zuma

Shugaba Jacob zuma Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Jacob Zuma na cigaba da fuskantar matsayin lamba don ya sauka daga kan mulki

Babbar kungiyar kwadago ta Afirka ta Kudu mai karfin fada aji ta Cosatu, ta bukaci Shugaba Jacob Zuma ya sauka daga kan mulki.

Sakatare Janar na kungiyar Bheki Ntshalintshali ya ce a yanzu, "ba shi ne" ya dace ya mulki kasar ba.

Mista Zuma ya dade yana fuskantar matsin lamba bayan ya yi wasu muhimman sauye-sauye a majalisar ministocin kasar, inda ya kori ministan kudi Pravin Gordhan, wanda ke da matukar kima.

Lamarin ya sa ana kallon kasar a matsayin wacce ba lallai bane ta iya biyan basusukan da ake bin ta ba kuma hakan ya kara saka tattalin arzikinta cikin matsi.

Kungiyar kwadagon, wadda wani muhimmin bangare ne na hadakar da ke mulki ta ce tana da mambobi kusan miliyan biyu.

'Yan jam'iyyar komunisanci ta SACP ma sun bukaci shugaban ya sauka.

Wa'adin mulkin Mista Zuma a matsayinshin shugaban kasa karo na biyu zai kawo karshe ne a shekarar 2019.

A makon da ya gabata ne mataimakin shugabana kasar, Cyril Ramaphosa, ya kira korar Mista Gordhan a matsayin abin da ba za a "amince da shi ba kwata-kwata".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Korar Mista Gordhan da Shugaba Zuma ya yi ita ce ta jawo wannan lamarin

Daga baya, a wani jawabi da yayi a karshen makon da ya gabata, ya bukaci a sabunta kasar inda ya soki mutane masu "karbar hanci da son kansu".

Shi ma tsohon shugaban kasar, Kgalema Motlanthe ya ce zai yi wuya a bi wani umarni da Mista Zuman zai bayar bayan kotun tsarin mulki ta kama shi da saba doka a lokacin da yaki biyan gwamnati kudadenta da aka yi amfani da su wajen gyara gidanshi.

Wakilin BBC, Milton Nkosi da ke birnin Johannesburg, ya ce an sha hasashen cewa ta Mista Zuma ta zo karshe, amma sai shugaban ya kai labari daga baya.

Duk da ce-ce-ku-cen da ya dabaibaye gwamnatinsa, an sha yunkurin tsige Mista Zuma daga kan mulki ba tare da anyi nasara ba.

Labarai masu alaka