Saɓon Allah ne ya jawo sanƙarau — Gwamna Yari

Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari Hakkin mallakar hoto Premium Times
Image caption Gwamna Yari ya ce akwai bukatar mutane su koma ga Allah

A ranar Talata ne dai gwamnan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, Abdul'aziz Yari ya ce saɓon Allah da ake yi ne ya jawo annobar sanƙarau da ake fama da ita a ƙasar.

Gwamna Yari ya furta wadannan kalaman ne a lokacin da ya ke gabatar da wani jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya yi jawabin ne bayan ya yi wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.

Zamfara ce Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake bai wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.

A makon da ya gabata ne Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar, ta soki gwamnatin Zamfaran a kan gazawarta wajen shirya wa barkewar annobar duk da gargadin da aka rika bayarwa.

A hannu guda kuma gwamna Yari ya ce barkewar annobar ba zai rasa nasaba da rashin biyayyar da mutane ke yi wa Allah ba a wannan lokaci.

Ya ce, "Mutane sun ƙauracewa Allah kuma ya yi alkawarin cewa idan ka yi ba daidai ba to kuwa zaka ga ba daidai ba, kuma ni dai a iya tunanin na wannan shine dalilin da yasa ake fuskantar wannan annobar".

Gwamnan ya kara da cewa babu yadda za a yi a ce zina ta yi yawa kuma Allah ba zai saukar da annobar da babu maganinta ba.

Ga dai tsokacin da gwamnan ya yi a wata hira da manema labari:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Yari kan batun Sankarau

Labarai masu alaka