Amurka ta janye tallafin tsarin iyali a kasashe 150

Saliyo Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption Hukumar ta UNFPA na inganta harkokin kiwon lafiyar mata da tasin iyali a Saliyo.

Amurka ta ce za ta janye kudaden tallafi da take bai wa Asusun Kidayar Jama'a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA, hukumar da ke kokarin ganin an yi amfani da tsarin kayyade iyali a kasashe fiye da 150.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce hukumar na goyon baya da kuma taka rawa a wani shirin zubar da ciki ko hana daukar ciki a China.

Sai dai hukumar UNFPA ta ce wannan ''kage ne'', kuma aikinta bai karya wata dokar Amurka ba.

A shekarar 2017 za a janye kimanin dala miliyan 32.5 da ake bai wa hukumar UNFPA a matsayin tallafi.

Wannan ita ce janyewar tallafin kudi da ake bai wa Majalisar Dinkin Duniya ta farko da gwamnatin Mista Trump ta yi alkawarin yi.

Hukumar UNFPA kamar sauran hukumomin Majalisar Dinkin Duniya na samun gudunmowa daga gwamnatin kasashe da dama ne.

A shekarar 2015, ta samu gudumuwar dala miliyan 979, inda Amurka ta zama kasa ta hudu da ta bayar da gudunmuwa mafi girma.

''Kage''

A farkon wannan shekarar ne, shugaba Donald Trump ya sake jaddada aniyarsa ta janye kudaden da Amurka take bai wa duk wata kungiya ta kasa da kasa da take goyon bayan zubar da ciki ko bayar da shawara kan hakan.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta dauki wannan mataki don cika umarnin da aka bayar a watan Janairu da kuma sauyin da aka samar kan lamarin.

Ta kuma ce, "An yi hakan ne saboda har yanzu a China ana tilasta mutane wajen zubar da ciki, kuma UNFPA tana hada gwiwa da gwamnatin Chinar kan ayyukan da suka shafi wadannan al'amura."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jakadar Amurka zuwa Majilisar dinkin duniya Nikki Haley ke kula da janye kudade zuwa ga majalisar.

Hukumar ta UNFPA ta ce wadannan zarge-zarge duk ''kage ne'' kuma duk aikin da take yi na kare hakkin jama'a ne da ma'aurata ta hanyar barin su su dauki matakin da ya yi musu, ba tare da an takura musu ko kuwa nuna bambanci ba.''

Hukumar ta kara da cewa shirye-shiryenta na kare rayuwar dubban mata. Ayyukanta sun hada da:

  • Taimakawa mata da matasa samun taimakon ayyukan haihuwa da kayyade iyali.
  • Hana daukar ciki ba tare da shiri ba da kuma zubar da ciki.
  • Tallafawa masu juna biyu ta hanyar kiwon lafiya.
  • Gudanar da shirye-shirye a kasashen duniya masu rauni kamar Iraki da Sudan ta Kudu da Syria da Yemen da kuma Somaliya.

Wakiliyar BBC a birnin New York, Nada Tawfik, ta ce dama gwamatin jam'iyyar Republican mai rikau na hakon Asusun Kidayar Jama'a na Majalisar Dinkin Duniya.

Shugabannin da suka yi mulkin kasar karkashin jam'iyyar Republican kamar su Ronald Reagan da George HW Bush da kuma George W Bush sun janye irin wadannan tallafi saboda wadannan dalilai.

Ma'aikatar harkokin wajen Amukan ta ce za a karkata kudaden da aka kasafta da niyyar bai wa UNFPA na shekara 2017, zuwa shirin kiwon lafiya na duniya.

Hukumar taimako ta kasa da kasa ta Amurka wato USAID, za ta yi amfani da wadanan kudade wajen tallafawa ayyukan da suka shafi tsarin kayyade iyali da masu juna biyu da kuma masu haihuwa a kasashe masu tasowa.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba