Theresa May ta kai ziyara Saudiyya

Sarki Salman na masarautar Saudi Arabia Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saudiyya na son tabbatar da cewa ta kulla kyakkyawar dangantakar tsaro tsakaninta da Birtaniya

Firai Ministar Birtaniya, Theresa May ta kai ziyara Saudiyya ranar Talata, ta tsawon kwana biyu.

Saudiyya ce kasar da Biritaniya ta fi karfin dangantakar kasuwanci da ita a kasashen Larabawa.

Wannan ziyara da Birtaniya ke kai wa, ta ta'allaka ne kacokan kan kara kulla dangantakar kasuwanci, a yayin da kasar ke neman madafa bayan ficewar ta daga kungiyar Tarayyar Turai, EU, musamman ta fannin zuba jari.

An lissafa jumlar saye da sayarwa tsakanin Saudiya da Birtaniya da cewa ya kai fam biliyan 6.6 a shekarar 2015.

Ga masarautar Saudiyya dai, wacce ke daya daga cikin daidaikun masarautu da suka rage a duniya, ziyarar na da wata manufar kuma daban.

Saudiyya dai na ci gaba da fuskantar barazanar aukuwar hari daga sojojin makwabtanta Iran, ganin yadda taswirar Gabas Ta Tsakiya ke nuna Iran din ta baza iko da biranen Tehran da Bagadaza da Damsacus da Beirut da kuma Sana'a, tana kuma kan hada kan mabiya mazhabar Shi'a a Bahrain da gabar tekun Persia, ta bangaren Saudiyya.

Wannan shi ne dalilin da ya sa Saudiyyar ke neman tabbatar da cewa dangantakarta ta fannin tsaro, na da karfi sosai tsakanin ta da Biritaniya da ma Amurka.

Labarai masu alaka