'Rabuwata da abokin zamana ta sa na so kashe kaina'

Wani mara lafiya a Ghana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A cikin `yan makonnin nan an samu rahoton wadanda suka yi yunkurin kashe kansu kamar goma a kasar Ghana.

Masana a Ghana suna bayyana damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar masu yunkurin kashe kansu a ƙasar, abin da ya sa hukumomi ke ba da lambar waya ta musammam don taimaka wa masu yunƙurin.

A cikin `yan makonni an samu rahoton cewa wadanda suka yi yunkurin kashe kansu sun kai mutum goma.

Wannan lamari ya sanya hukumar kula da masu taɓin hankali ta Ghana buɗe wani layin wayar tarho na kiran gaggawa da nufin ba da taimako.

Hukumar lafiya ta duniya dai ta ce duk lokacin da aka samu wanda ya kashe kansa ko wadda ta kashe kanta, akwai mutum,20 da suka yi yunkurin kashe kansu.

Babu dai takamaiman bayanai kan adadin wadanda suka yi yunkurin kashe kan nasu a faɗin kasar, abin da ya sa da wuya a san haƙiƙanin yawan mutanen da suka kashe kansu ya zuwa yanzu.

Wahalar samun bayanai

Yunƙurin kashe kai babban laifi ne a dokar kasar Ghana, don haka ba kasafai mutane ke kai ƙorafi ta yadda za a iya taikama wa mutanen da abin ya shafa cikin sauƙi ba.

Hilda Brown mai shekaru 32, wata injiniyar hada sinadarai ce da ta shiga irin wannan hali na yunkurin kisan kanta.

''Mun samu saɓani bayan shafe tsawon lokaci da abokin zamana, wannan ta kai mu ga rabuwa, na shiga halin ƙunci sosai, don haka sai na yi yunkurin kashe kaina.''

Bayanai sun ce daga shekara ta 2008 zuwa 2011 babu yawan matsalar kashe kai da kai a Ghana, amma cikin yan makonnin baya-bayan nan an samu sama da mutum goma da suka kashe kansu.

Ita ma Linda Enchwi mai shekaru 30 ta damu saboda ɗan'uwanta ya kashe kansa shekara shida da ta gabata, abin da ke dugunzuma 'yan gidansu har yanzu.

'' Shi kaɗai ne ɗa namiji a wajen mahaifinmu, kuma har yanzu abin yana cin ransa, yakan je kan kabarinsa ya yi ta juyayi. Kuma duk lokacin da na ji wani ya kashe kansa, sai ɗan'uwana ya faɗo min a rani na fara tunanin abin da ya same shi.''

Labarai masu alaka