An gano manyan kaburbura a Jamhuriyar Congo

Jamhuriyar Dimokradiyyar Comgo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Jamhuriyar Congo din sun jima suna fafatawa da kungiyar masu tada kayar baya a yankin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano manyan kaburbura 13 a lardin Kasai na Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, tun daga farkon watan Maris.

Hakan ya kai yawan adadin da aka gano zuwa 23 tun daga watan Agustar bara.

Majalisar Dinkin Duniyar ta gaza tantance manyan kaburburan, kana ba za ta iya bayyana ko sabbi bane.

Ta kiyasta cewa mutane sama da 40 ne da suka hada da mata da kananan yara aka hallaka a fada tsakanin dakarun kasar da kuma kungiyar 'yan tawaye.

Jose Maria Aranaz, daraktan gamayyar ofishin lura da kare hakkin biladama na Majalisar Dinkin Duniya, ya shaidawa BBC cewa yana da muhimmanci a gudanar da sahihin bincike, don tabbatar da yawan al'umma, da kuma ganin cewa an hukunta masu aikata ta'asar.

Gwamnati na fadi tashin ganin ta murkushe kungiyar 'yan tawayen da ake kira Kamwina Nsapu, da ta bullo tun bayan kisan shugaban yankin Kasai.

Ana dai zargin duka bangarorin biyu da saba dokar kare hakkin biladama.

A watan da ya gabata ne aka sace kwararru biyu na Majalisar Dinkin Duniyar, lokacin da suke gudanar da aikin bincike kan cin zarafin biladama a yankin na Kasai, inda aka gano su a wasu kabarurruka marasa zurfi.

Dakarun Jamhuriyar Congo din sun jima suna fafatawa da kungiyar masu tada kayar baya a yankin.

Labarai masu alaka