Amurka ta zargi Syria ta aikata gagarumin rashin imani

Kasar Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akasarin wadanda suka mutu a harin iska mai gubar kananan yara ne

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, ya zargi gwamnatin kasar Syria da aikata mugunta, bayan harin iska mai guba da ake zarginta da kai a lardin Idlib da ya hallaka akalla mutane 58.

Bayan hari ta sama kan garin Khan Shiekhoun a lardin na Idlib , an bada rahoton cewa daruruwan mutane akasari kananan yara na ta hararwa, da shakewa da kumfar baki.

Fadar White House ta ce tana da yakinin cewa gwamnatin shugaba Bashar na da alhakin kai harin makamai masu gubar da ya hallaka mutane akalla 58 a arewa maso yamamcin Syria.

Hukumar da ke sa ido kan kare hakkin biladama ta kasar Syria ta bada rahoton cewa harin da dakarun gwamnatin Syria ko jiragen yakin kasar Russia suka kai kan garin Khan Sheikhoun ya sa mmutane da dama sun kware.

Masu fafutika na kasar Syriyar sun ce daga bisani wani jirgin yaki ya harba rokoki kan wasu kananan asibitocin yankin da ke duba lafiyar wadanda harin ya shafa magani.

Rundunar sojin kasar ta Syria ta musanta cewa gwamnati ta yi amfani da makamai masu gubar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shaidu sun ve kananan asibitoci da ke kula da wadanda suka jikkata na fuskantar barazanar hari ta sama

A wata sanarwa, shugaban Amurka Donald Trump ya yi tur da harin da ya kira '' Rashin imani da tausayi'' na gwamnatin Bashar al-Assad.

Amma kuma ya zargi gwamnatin tsohon shugaba Barack Obama wajen gaza hukunta kasar ta Syria kan harin makamai masu guba na shekara ta 2013.

Hukumar da ke sa ido kan makamai masu guba ta kasa da kasa, OPCW, ta ce tana kan tattara shaidu.

Ralf Trapp tsohon babban jami'an hukumar ne.

"Na fahimci cewa an fitar da wasu mutanen zuwa Turkiyya. Kamar yadda muka gane a baya idan ka samu samfurin jini da wasu gwaje-gwajen halittun jiki a cikin ɗan lokaci ko 'yan kwanaki ana iya tabbatar da ko an yi amfani da sinadarin Sarin."

Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Birtaniya da Faransa da sauransu, sun yi Allah wadai da wannan mataki, wanda muddin aka tabbatar zai kasance harin makamai masu guba mafi muni a tarihin yakin basasar kasar Syria.

Labarai masu alaka