'Sai 'yan sanda sun sani za ka yi budurwa'

Kylle Godfrey Hakkin mallakar hoto METROPOLITAN POLICE
Image caption Ana iya ɗaure Godfrey matuƙar ya saɓa wa wannan umarni

Kotu ta umarci wani mutum da ya yi "mummunar" ƙuntatawa ga tsohuwar abokiyar zamansa, ya riƙa sanar da 'yan sanda a duk lokacin da ya yi sabuwar budurwa.

Umarnin ya buƙaci Kylle Godfrey, ɗan shekara 30, da ke yankin Neasden a arewa maso yammacin London ya sanar da 'yan sanda idan ya yi sabuwar budurwar da suka daɗe sama kwana 14 nan da shekara bakwai masu zuwa.

Yanzu dai Kylle Godfrey yana zaman gidan yari tsawon shekara uku saboda cin zarafin tsoffin abokan zamansa biyu da kuma razana wani shaida a lokacin da aka ba shi beli.

An yi imani umarnin shi ne irinsa na farko a Ingila da Wales.

A wani ɓangare na umarnin, 'yan sanda ka iya faɗa wa abokiyar zaman Godfrey ta gaba game da halayyarsa ta cin zarafin mata a baya.

A baya ma, an taɓa samun wani John O'Neill daga yankin York wanda shi ma aka buƙaci ya riƙa faɗa wa 'yan sanda idan ya yi sabuwar abokiyar zama.

Tun ranar 14 ga watan Fabrairu ne aka tsare Godfrey bayan samun shi da laifi biyu na yi wa wata rauni da karkatar da hankalin shari'a da kuma cusguna wa shaida.

Kotu ta saurari yadda Godfrey a tsawon kwanaki cikin watan Oktoban bara, ya riƙa far wa abokiyar zamansa, yana gwara kanta da bango da kuma makure ta.

Bayan kama shi, Godfrey ya ci gaba da musgunawa matar, kuma a lokacin da yake kan beli ya sake cin zarafin wata mace da ya fara hulɗa da ita.