Helikwafta ya tafi neman yaron da ke ƙarƙashin gado

A School Boy Josh Dinning

Asalin hoton, GLEN MINIKIN

Bayanan hoto,

Josh Dinning ya wayi gari ranar Litinin amma ba ya son zuwa makaranta don ya ɓuya a ƙarƙashin gado

An gano wani yaro ɗan shekara 9 ɓoye a ƙarƙashin gado bayan 'yan sanda sun bazama nemansa a Ingila, lokacin da mahaifiyarsa ta wayi gari ba ta gan shi ba.

'Yan sanda sun auka wani kogi da nema baya ga wani helikwafta da ya runtuma sama a ƙoƙarin gano inda Josh Dinning, daga Gateshead ya shiga, tun cikin daren Litinin.

'Yan sanda sun shafe tsawon sa'a uku suna nema, amma ba su ga Josh Dinning ba.

Asalin hoton, GLEN MINIKIN

Bayanan hoto,

Josh ya takure a cikin wannan loka ta ƙarƙashin gado tsawon sa'a ana nema

Sai daga bisani ne aka gano shi ƙunshe a cikin loka a ƙarƙarshin gadonsa. Ya ce ba ya son zuwa makaranta ne a ranar.

Mai magana da yawun 'yan sanda a Northumbria ya ce rundunarsu na nazari kan dalilin da ya sa ba a duba "lokar ta ƙarƙshin gado ba".

Mahaifiyarsa, Michelle Dinning, bazawara mai 'ya'ya takwas ta ce ta yi tsammanin Josh yana makaranta lokacin da ba ta gan shi ba.

Sai dai, makarantar ta buga mata waya ta sanar da ita ce cewa ba a ga Josh ba, dalilin da ya sa ta kira 'yan sanda.

Ta ce, "A wannan lokaci sai na shiga taitayina, duk na kaɗu, ina tunanin ko wani mummunan al'amari ne ya faru."

Asalin hoton, GLEN MINIKIN

Bayanan hoto,

Josh ya yi lamo a tsawon lokacin da ake nema don ya san idan aka gan shi za a ja masa kunne

Batun ɓatan Josh ya sa maƙwabta sun shiga inda suka riƙa raba hotunansa da aka buga.

Mahaifiyarsa ta ce: "Sai na ce kai a sake duba cikin gida mana - wannan karon sai 'yan sanda suka ɗaga gado.

"Ina leƙa wa sai na hango koriyar rigar makarantar Josh, ai sai na ɓarke da kuka."