Harin bam ya hallaka jami'an ƙidaya a Pakistan

Pakistani security officials collect evidence from the scene of a suicide bomb attack on a census team in Lahore on April 5, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fiye da mutum 20 ne harin ya jikkata

A kalla mutum shida ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake kyautata zaton na kunar bakin wake ne, wanda aka kai wa masu aikin ƙidaya da kuma jami'an tsaron da ke musu rakiya a birnin Lahore na ƙasar Pakistan.

Hukumomi sun ce mutum huɗu cikin waɗanda suka mutu sojoji ne, yayin da wasu mutum 22 sun jikkata.

'Yan sanda sun ce ma'aikatan da suke aikin kidayar aka nufa da harin, wadda ita ce ta farko a tsawon shekara 20.

Wannnan harin yana zuwa ne bayan jerin wasu hare-hare da kungiyar Taliban da ke Pakistan din ta dauki alhakin kai wa a makonnin da suka gabata.

Ko harin na ranar Larabar ma, kungiyar Taliban din ce ta dauki alhakin kai shi.

An dai killace wurin da aka kai harin don fara gudanar da bincike.

Sai dai ba za a iya tabbatar da cewa ko fararen hular biyu da suka mutu ma'aikatan da ke aikin ƙidayan ne, ko kuma 'yan kallo ba.

Masu ikirarin kafa daular Musuluncin na kungiyar Taliban suna yawan kai wa jami'an tsaro hari a kasar.

A wata sanarwa da Kungiyar Taliban din ta fitar, ta ce harin na daukar fansa ne a kan jami'an tsaro.

'Yan Taliban din suna ci gaba da kai hare-hare ne bayan farmakin da sojoji suke kai wa a arewa-maso-yammancin ƙasar.

A watan Fabrairu, wani bangare na Kungiyar Taliban ya dauki alhakin kai wani hari a birnin Lahore, inda mutum 13 suka rasa rayukansu wasu kuma fiye da 80 suka jikkata.

'Yan kwanaki bayan haka ne kuma aka kai wani harin kunar bakin wake a wani hubbare a garin Sehwan da ke kudancin kasar, wanda Kungiyar IS ta dauki alhakin kai wa. Mutum 90 ne suka rasa rayukansu a harin kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Labarai masu alaka