DR Congo: Ba ma son sa idon kasashen waje a zaben kasarmu

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaba Kabila ya fara mulki ne a shekarar 2001

Shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Joseph Kabila ya ce ba zai bar kasashen waje su sa baki ba a babban zaben kasar mai zuwa.

Ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP a babban birnin kasar Kinshasa, cewa nan da sa'o'i 48 masu zuwa zai bayyana sunan sabon Firayim ministan kasar, wanda zai jagoranci kasar domin gudanar da zaben.

Masu suka dai na ganin cewa ya jinkirta gudanar da zaben ne saboda ya ci gaba da zama akan karagar mulki.

Wa'adin mulkin Mista Kabila na biyu kuma na karshe ya zo tun karshen shekara da ta gabata, amma kuma ba a yi zabe ba.

Hukumar zaben kasar dai ta ce rashin kudi, da kuma shiri ne suka hana ta gudanar da zaben.

Rashin gudanar da zaben dai ya haifar da zanga-zangar 'yan adawa wanda hakan ya janyo mutuwar mutane, tare da kiraye-kiraye daga ma'aikatan diflomasiyya cewa Mista Kabila ya girmama kundin tsarin mulki.

Sai dai Cocin Katolika ya kawo wata shawara a karshen shekarar da ta gabata, wacce ta ce a kafa gwamnatin rikon kwarya wanda zai hada da 'yan adawa domin kula da zaben.

Amma kuma shawarar ba ta samu karbuwa ba saboda gwamnati da 'yan adawan, duk sun ki amincewa da raba iko kamar yadda shawarar ta nuna.

Da yake mayar da martani ga shugaban Cocin Mista Kabila, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Mps cewa zaben zai gudana kamar yadda aka tsara.

Mista Kabila ya ce "Ina so ina sanar da mutanenmu cewa za a gudanar da zabe. Ga wadanda suke da shakku za mu fito da jadawalin zabe domin mu kawar da shakkunsu".

"Wannan aiki ne na mutanen Congo, kuma da kudin mutanen Congo za a yi, ba tare da sa bakin kasashen waje ba"

Jawabin na Mista Kabila na zuwa ne kwanaki kadan, bayan kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya kada kuri'ar rage karfin shirinsa na wanzar da zaman lafiya a kasar watau Monusco.

Kafin kuri'ar dai sai da wakiliyar Amurka a majalisar dinkin duniya Nikki Hailey ta zargi kungiyar da kawance da gwamnatin Kabila wacce ta kira da gwamnatin masu cin hanci,