Nigeria ta fara rigakafin cutar sankarau

Ma'aikatan kiwon lafiya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sama da mutum 300 sun rasa rayukansu a Najeriya sakamakon annobar tun a bara.

Ma'aikatan kiwon lafiya a Najeriya sun fara rigakafin cutar sankarau a wani yunkurin na dakatar da cu gaba da yaduwar cutar.

Sama da mutum 300 sun rasa rayukansu sakamakon annobar tun a bara.

Ma'aikatan na mayar da hankulansu kan jihar Zamfara da ke arewa-maso gabashin kasar, inda nan ce cibiyar barkewar annobar.

Cibiyar shawo kan cututtuka ta Najeriya ta ce za a yi rigakafi ga mutum 500,000.

Jami'an kiwon lafiya sun ce akwai kusan mutum 3,000 wadanda ake zaton suna fama da annobar sankarau.

Kawo yanzu, annobar ta fi shafar yara masu shekara tsakanin biyar zuwa 14.

Wani jami'i ya shaida wa BBC cewa rashin allurar rigakafi ne ya sa ba a mayar da hankali sosai kan shawo kan annobar ba.

Nau'in cutar sankarau da aka sani da "meningitis type C" wanda ba a saba samun aukuwar shi a Najeriya ba ne ya jawo barkewar annobar.