Kun san a Burtaniya ma ana auren kisan wuta?

Hannu wata mai kunshi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A wasu lokutan ana ci da gumin matan dake yin irin wannan auren

Mata kan biya kudi su yi aure domin su sadu da maza sannan daga bisani a sake su domin su koma ga mazansu na farko.

Farah - wadda ba sunanta na gaskiya ba ne - ta hadu da mijinta ne bayan wata 'yar uwarta ta hada su a lokacin tana da shekara 20.

Bayan an yi auren ta haihu sai ya fara cin zarafinta.

"Da farko dai a kan kudi ya ci mini mutunci," kamar yadda ta shaida wa sashen BBC na Asiya da kuma shirin BBC na Derbyshire.

Ta kara da cewa "Ya kama gashina ya yi ta jana a kasa yana shiga dakunan gidan yana fitowa kuma ya yi kokarin korata daga gidan. A wasu lokutan kuma tamkar ya haukace".

Duk da cin zarafinta da yake yi, Farah ta sa ran abubuwa za su sauya.

Amma kuma sai abubuwa suka kara tabarbarewa inda har ya aika mata da sakon saki ta wayar tarho a rubuce.

"Ina gida tare da yara shi kuma yana wurin aiki. Bayan mun yi wata jayayya mai zafi sai ya aiko mini da sako a rubuce ta wayar tarho yana cewa 'talaq, talaq, talaq."

Farah ta ci gaba da bayani kamar haka "A lokacin wayata tana hannu na sai kawai na mika wa mahaifina. Sai ya ce aurenki ya mutu ba zaki koma gidanshi ba."

Farah ta ce ta "Dimauce kuma ta shiga tsananin damuwa", amma kuma tana fata ta koma ga tsohon mijinta saboda shi ne mutumin da take so. Ta kara da cewa shi ma ya yi nadamar sakinta da yayi.

Wannan ne yasa Farah ta yi tunain yin auren Halala.

Duk da dai Musulunci bai halasta irin wannan auren ba, mutane da dama sun yi amannar ita kadai ce hanyar da wadanda aurensu ya mutu kuma suke so su koma za su iya bi domin cimma burinsu.

A auren Halala, matar za ta auri wani mutum daban daga baya kuma sai ya sake ta daga nan kuma za ta iya koma wa ta auri mijinta na farko.

Amma a wasu lokutan, ana ci da gumin matan da ke yin irin wannan auren ko ma a ci zarafinsu.

Abu ne da Musulunci ya haramta kuma ana danganta masu yin shi da rashin fahimtar ka'idojin saki a addinance.

Wani binciken da BBC ta yi ya gano shafukan intanet da dama da ke bai wa mata damar yin auren Halala, inda mata da dama ke biyan dubban fama-famai domin su yi auren.

Matsuwa

Image caption Khola Hasan ta jadadda cewa Musulunci ya haramta auren Halala

Wani mutum, mai yin tallan auren halala a shafinsa na Facebook, ya shaida wa wata wakiliyar BBC da ta je wurin shi a matsayin bazawara cewa sai ta biya fam 2,500 kuma ta yi jima'i da shi kafin auren ya halasta kuma daga baya sai ya sake ta.

Mutumin ya kara da cewa akwai maza da dama da suke yin irin wannan auren, inda ya ce daya daga cinkinsu ma yaki ya saki matar bayan an yi auren halalan.

Amma kotun Shari'a da ke gabashin London, wanda ke bayar da shawarwari kan mace-macen aure, ya yi tur da auren halala.

"Wannan aure abin takaice ne, aure ne da mutane ke yi domin su samu kudi kuma su ci zarafin wadanda abin ya shafa." A cewar Khola Hasan dake aiki a kotun.

Ta kara da cewa "Musulunci ya haramta shi. Babu kalmar da zan iya amfani da ita domin na nuna girman haramcin wannan lamari."

"Ba za mu amince da irin wannan ba. Babu wanda yake bukatar halala, ko ma wani rin hali ka tsinci kanka a ciki."

Daga baya Farah ta sauya tunani a kan auren halala da kuma hadarin da ke tattare da komawa wajen tsohon mijinta.

Amma ta yi gargadin cewa akwai mata da dama kamarta da ke neman mafita.

"Idan har baka tsincin kanka a cikin halin da nake ciki ba, mutum ba zai taba fahimtar irin halin kuncin da mata ke fuskanta ba."

Labarai masu alaka