Ba saɓon Allah ne ya janyo sanƙarau ba — Sarki Sanusi

Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari Hakkin mallakar hoto Premium Times
Image caption Gwamna Yari ya ce akwai bukatar mutane su koma ga Allah

Mai martaba Sarki Kano Muhammadu Sanusi II ya soki gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari a kan kalaman da ya yi cewa sabon Allah ne ya haddasa cutar sankarau a jiharsa.

Da yake jawabi a wurin wani taro kan zuba jari da aka yi a Kaduna, Sarki Sanusi ya ce bai kamata mutum mai mukami irin na gwamna ya rika alakanta abin da ya shafi kiwon lafiya da sabon Allah ba.

A cewarsa, "Mutum sama da 200 sun mutu, an tambayi gwamna amma ya ce wai sabon Allah ne ya sanya hakan. Bai kamata a rika yin irin wannan jawabi ba. Wannan kalami da {yari} ya yi bai yi daidai da koyarwar Musulinci ba."

"Idan ba shi da maganin rigakafin sankarau, sai kawai ya je ya nemo", in ji mai martaba Sarkin na Kano.

A ranar Talata ne dai Gwamna Abdul'aziz Yari ya ce saɓon Allah da ake yi ne ya jawo annobar sanƙarau da ake fama da ita a ƙasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya yi jawabin ne bayan ya yi wata ganawa da shugaban kasar Muhammadu Buhari a kan batun.

Zamfara ce Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake bai wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.

A makon da ya gabata ne Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar, ta soki gwamnatin Zamfaran a kan gazawarta wajen shirya wa barkewar annobar duk da gargadin da aka rika bayarwa.

A hannu guda kuma gwamna Yari ya ce barkewar annobar ba zai rasa nasaba da rashin biyayyar da mutane ke yi wa Allah ba a wannan lokaci.

Ya ce, "Mutane sun ƙauracewa Allah kuma ya yi alkawarin cewa idan ka yi ba daidai ba to kuwa zaka ga ba daidai ba, kuma ni dai a iya tunanin na wannan shine dalilin da yasa ake fuskantar wannan annobar".

Gwamnan ya kara da cewa babu yadda za a yi a ce zina ta yi yawa kuma Allah ba zai saukar da annobar da babu maganinta ba.

Ga dai tsokacin da gwamnan ya yi a wata hira da manema labari:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Yari kan batun Sankarau

Labarai masu alaka