APC ta ja kunnen jami'an gwamnatin Buhari

Buhari da Saraki Hakkin mallakar hoto Senate
Image caption An dade ana takun-saka tsakanin bangaren zartarwa da na 'yan majalisa

Jam'iyyar APC da ke mulkin Najeriya ta gargadi wasu jami'an gwamnatin Muhammadu Buhari a kan kalaman da suke yi wadanda ke dada kawo sabani tsakanin bangaren zartarwa da 'yan majalisar dokokin tarayya.

Jami'iyyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta Mallam Bolaji Abdullahi ya aike wa manema labarai.

APC ta yi wannan gargadi ne saboda caccakar da shugaban kwamitin da ke bai wa shugaban kasa shawara kan yaki da cin hanci da rashawa Farfesa Itse Sagay ke yi wa majalisar dattawan kasar.

Farfesa Sagay dai yana sukar majalisar dattawan ne saboda, a cewarsa, ba ta kaunar yaki da cin hanci da rashawar da Shugaba Buhari ke yi shi ya sanya ta ki tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC, da ke yaki da masu yi wa tattali arzikin kasa ta'annati.

Sai dai sanarwar da Mallam Bolaji ya fitar ta ce APC ta ja kunnensa ne saboda yunkurin da take yi na kyautata dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da na masu yin dokoki.

A cewarsa sanarwar, "Jam'iyyar APC tana kira ga dukkan mutanen da gwamnatin nan ta nada da su daina yin kalaman da za su ci gaba da kawo cikas a dangantakar da ke tsakanin bangarorin gwamnati guda biyu domin kada su yi kafar-ungulu ga yunkurin da jam'iyya ke yi na tabbatar da zaman lafiya tsakaninsu".

"Mun yi amannar cewa kalaman da aka ambato Farfesa Sagay na yi ba su dace ba, kuma abin takaici ne da za su iya dagula dangantakar da ke tsakanin wadannan bangarori na gwamnati," in ji APC

Labarai masu alaka