Za ka auri macen da ka yi wa fyaɗe?

Shabudin Yahaya ya ce babu laifi idan mace ta auri wanda ya yi mata fyade Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shabudin Yahaya ya ce babu laifi idan mace ta auri wanda ya yi mata fyade

Wani dan majalisar dokokin Malaysia ya gamu da fushin jama'a saboda ya ce babu laifi idan mutum ya auri macen da ya yi wa fyade kuma akwai mata 'yan shekara 12 da suka shirya tsaf domin zama matan aure.

Shabudin Yahaya na jam'iyyar Barisan Nasional coalition mai mulki, ya ce yin aure zai taimakawa matan da aka yi wa fyade "yin rayuwa mai kyau".

Malaysia kasa ce da Musulmi suka fi rinjaye, kuma kwanan baya ta zartar da sabuwar dokar yin hukunci ga duk wanda ya yi lalata da kananan yara.

Sai dai dokar ba ta hana auren kananan yara ba.

Ba laifi ba ne idan aka aurar da yarinya 'yar shekara 16 a karkashin dokar Malaysia.

'Shawo kan matsalolin da suka addabi al'uma'

Mr Shabudin, wanda ya bayar da tasa gudunmawar a muhawarar da 'yan majalisar suka yi kan kudirin dokar, ya ce koda yake fyade babban laifi ne, amma ya kamata a ba da dama ga duk macen da aka yi wa fyade ta sake sabuwar rayuwa.

"Ina ganin idan macen da aka yi wa fyade ta yi aure za ta gudanar da rayuwa mai kyau," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan majalisar, wanda ba ya cikin wannan hoton, dan jam'iyyar Firai Minista BN ta Fira Minista Najib Razak (na dama) ne

Sai dai daga bisani ya ce an yi wa bayaninsa gurguwar fahimta.

A kasar Malaysia, ana ta kiraye-kiraye domin yin aiki da dokokin Musulinci sau da kafa.

Labarai masu alaka