An tuhumi Diezani kan maguɗin zabe

Diezani Alison-Maudeke Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba wannan ne karon farko da Diezani Alison-Maudeke ke samun kanta cikin zargin badakala ba

Wata kotun Najeriya ta tuhumi tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Maudeke da wasu jami'an hukumar zaben kasar, INEC da laifin yin amfani da kudi da zummar murde zaben shekarar 2015.

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati ce dai ta gurfanar da jami'an INEC uku a gaban kotun tarayya da ke Lagos karkashin mai shari'a M. B. Idris, inda ta zarge su da karbar cin hanci N265m daga wurin Ms Alison-Madueke domin sauya sakamakon zaben 2015.

Jami'an INEC din da ake tuhuma su ne Christian Nwosu, Yisa Olanrewaju Adedoyin da Tijani Bashir.

Da yake jawabi a gaban kotun, Christian Nwosu ya amince da karbar cin hancin N30m daga tsohuwar ministar albarkatun man fetur din da zummar yin magudin zaben.

Diezani Alison-Maudeke ba ta kotu a lokacin da aka ayyana ta a cikin wadanda ake tuhuma da lafin halasta kudin haramun.

Tsohuwar ministar dai ba ta yi raddi kan wannan tuhuma ba, sai dai a baya ta sha musanta zarge-zargen da ake yi mata na cin hanci da rashawa.

Ms Alison-Madueke na daya daga cikin ministoci mafiya karfin fada-a-ji a gwamnatin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

Mr Jonathan ya sha kaye a hannun Muhamadu Buhari a zaben da aka yi a 2015.

Labarai masu alaka