Gwamnan Zamfara ya yi wa Sarki Sanusi raddi kan sanƙarau

Sarki Sanusi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarki Sanusi ya ce bai kamata shugabannin su rika yin magana irin ta Yari ba

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Abdul'aziz Yari, ya yi wa mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II raddi kan kalaman da ya yi cewa ba sabon Allah ne ya janyo annobar sankarau a Najeriya ba.

Shi dai Sarki Sanusi ya soki Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari a kan kalaman da ya yi cewa sabon Allah ne ya haddasa cutar sankarau a jiharsa.

Da yake jawabi a wurin wani taro kan zuba jari da aka yi a Kaduna ranar Laraba, Sarki Sanusi ya ce bai kamata mutum mai mukami irin na gwamna ya rika alakanta abin da ya shafi kiwon lafiya da sabon Allah ba.

A cewarsa, "Mutum sama da 200 sun mutu, an tambayi gwamna amma ya ce wai sabon Allah ne ya sanya hakan. Bai kamata a rika yin irin wannan jawabi ba. Wannan kalami da [Yari] ya yi bai yi daidai da koyarwar Musulinci ba."

"Idan ba shi da maganin rigakafin sankarau, sai kawai ya je ya nemo", in ji mai martaba Sarkin na Kano.

'Na yi mamakin kalaman Sarki'

Sai dai a wata hira da ya yi da BBC, Gwamna Yari ya ce, "Zan yi mamaki idan Sarkin Kano ya shiga sahun siyasa, ya ajiye karatu da ilimi. Na dogara ne da Al-Qur'ani da Hadisai kafin na yi kalamina. Na san Sarki ya san cewa ayoyi da yawa sun yi magana a kan cewa Allah zai saukar da bala'i ga al'uma idan tana aikata fasadi, musamman idan wadanda Allah ya bai wa ilimi sun kasa tashi su fadakar da al'uma".

"Saboda haka ne da aka tambaye ni a kan abin da muke yi domin shawo kan wannan cuta, sai na ce muna yin iya bakin kokarinmu. Amma na gargadi mutane cewa ya kamata su rika jin tsoron ubangiji idan ba haka ba Allah zai saukar musu da bala'i," in ji Gwamna Yari.

Gwamnan na jihar Zamfara ya kara da cewa bai kamata Sarki Sanusi ya caccake shi ba tun da ba shi ya kirkiro kalamin da ya yi ba, yana mai cewa "ko fada-fada na Coci ka tambaya za su gaya maka cewa zina da luwadi ba su da kyau. Kuma abin da na ce a daina kenan idan ba haka ba za a fuskanci bala'i kamar na wannan cuta. Sannan har gobe ina kan wannan matsayi."

Zamfara ce Jihar da annobar ta fi kamari tunda cutar ta barke, inda sama da mutum 200 suka mutu, kuma ake bai wa wasu da dama kulawa a asibitoci da cibiyoyin lafiya.

A makon da ya gabata ne kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar, ta soki gwamnatin Zamfaran a kan gazawarta wajen shirya wa barkewar annobar duk da gargadin da aka rika bayarwa.

Ga dai tsokacin da Gwamna Yari ya yi tun da farko a wata hira da manema labari:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar Yari kan batun Sankarau